Majalisa Ta Haramta Sanya Hijabi da Bukukuwan Murnar Sallah a Ƙasar Musulmi

Majalisa Ta Haramta Sanya Hijabi da Bukukuwan Murnar Sallah a Ƙasar Musulmi

  • Majalisar Majlisi Milli ta kasar Tajikistan ta amince da wani kudurin doka na haramta sanya hijabi ga mata musulmi a kasar
  • 'Yan majalisar sun ce hijabi "bakin tufafi" ne da ke da alaka da masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama
  • Gwamnatin Tajik karkashin jagorancin Emomali Rahmon ta zartar da kudirin dokar da ya haramta yara yin bukukuwan Sallah

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Tajikistan - Majalisar tarayyar Tajikistan ta amince da dokar hana sanya hijabi, da duk wani nau'i na lullubi da yawancin mata musulmi ke yi.

Gwamnatin Tajik karkashin jagorancin Emomali Rahmon ta zartar da kudirin dokar da ya haramta yara yin bukukuwan karama da babbar Sallah.

Kara karanta wannan

Hukuncin masarautar Kano ya lasawa bangarorin da ke rikici zuma a baki

Majalisar kasar Tajikistan ta haramtawa mata sanya hijabi
Tajikistan: An haramtawa mata sanya hijabi, yara kuma ba za su yi bukukuwan Sallah ba. Hoto: NurPhoto
Asali: Getty Images

An haramta sanya hijabi a Tajikistan

Tajikistan dai ta kasance kasar da ke da rinjayen musulmi wanda ke a tsakiyar Asiya kamar yadda jaridar The Cable ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar Majlisi Milli, babban zauren majalisar tarayyar kasar, ta amince da kudirin dokar a ranar Laraba, kimanin makonni biyu bayan da majalisar wakilai ta amince da kudirin.

'Yan majalisar sun ce hijabi "bakin tufafi" ne da ke da alaka da masu tsattsauran ra'ayin addinin Islama.

Jerin tarar da za ci masu karya doka

Jaridar Times Now ta ruwaito za a ci tarar duk wanda aka kama ya karya dokar daga somonis 7,920 (kimanin dala 745) ga daidaikun mutane zuwa somonis 39,500 (dala 3,718) ga ƙungiyoyin doka.

Jami’an gwamnati da hukumomin addini suna fuskantar tarar somonis 54,000 (dala 5,083) da somonis 57,600 (dala 5,422), idan aka same su da laifin karya dokar.

Kara karanta wannan

Babbar kotun tarayya ta yi hukunci kan dambarwar masarautar Kano

Tun a shekara ta 2007 ne hukumomin kasar Tajik suka dakile sanya hijabi a lokacin da ma'aikatar ilimi ta haramta wa dalibai saka suturar kasashen yamma.

An haramta sanya hijabi a Faransa

A wani labarin makamancin wannan, mun ruwaito cewa babbar kotun kolin Faransa ta yanke hukunci kan dokar hana sanya hijabi ga dalibai mata Musulmai.

Kungiyoyin Musulmai na Action for the Rights of Muslim da Council of the Muslim Faith sun shigar da kara domin kalubalantar wannan dokar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.