"Kun Wahalar da Alhazai, Gwamna Ya Ɗauki Zafi Yayin da Ya Yi Barazana ga NAHCON
- Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya koka kan yadda alhazai suka tsinci kansu a Saudiyya a bana
- Gwamnan ya soki tsarin hukumar NAHCON inda ya ce ya kamata a ba jihohi ragamar kula da alhazansu domin samar musu da walwala
- Legit Hausa ta tattauna da wani mahajjaci daga jihar Gombe kan tsare-tsaren hukumar kula da alhazai ts NAHCON
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Makkah, Saudiyya - Gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya caccaki hukumar alhazai ta kasa (NAHCON).
Bala ya nuna damuwa kan yadda hukumar ta ba mahajjatan kunya a Saudiyya ganin yadda ta ke tafiyar lamarin a bana.
Bauchi: Bala ya koka kan tsare-tsaren NAHCON
Sanata Bala ya bayyana haka ne yayin zantawa da mahajjatan jihar Bauchi a Mina da ke Makkah a kasar, cewar Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya bukaci gyara kan ayyukan hukumar domin samun sauyi a yadda take gudanar da ayyukanta, kamar yadda Punch ta tattaro.
Har ila yau, gwamnan ya bukaci a bar gwamnatocin jihohi su na kula da alhazansu tun da ta jiha suke biyan kudin aikin hajji.
Ya bayyana damuwa kan yadda mahajjata suka fuskanci wahalhalu saboda tsare-tsaren hukumar da sauran masu ruwa da tsaki.
Gwamna Bala ya yi barazana ga NAHCON
Tsohon Ministan ya ba da misalin yadda hukumar ta ba alhazai dala 500 a matsayin alawus na tafiye-tafiye duk da N8m da suka karba a hannun alhazan.
Daga bisani, gwamnan ya ce zai hada kai da sauran gwamnoni domin kwace ikon hukumar idan ba ta sauya tsarin da take tafiya a kai ba.
Sanata Bala ya yi amfani da wannan dama inda ya ba alhazan jiharsa 2,689 riyal 300 kowannensu a matsayin goron sallah.
Tattaunawar wakilin Legit Hausa da wani Alhaji
Legit Hausa ta tattauna da wani mahajjaci daga jihar Gombe kan tsare-tsaren hukumar NAHCON
Alhaji Muhammad Abdullahi ya ce shi ba yau ya fara zuwa ba amma a gaskiya an samu matsaloli da dama.
"Kullum kara inganta abubuwa ake yi a Saudiyya amma bana an dan samu matsaloli musamman daga ɓangaren hukumar NAHCON."
"Musamman yawan mace-mace da aka samu duk da ƙaddara ne daga Allah kuma ba iya Najeriya ba ne."
"Na ji wasu gwamnoni suna korafi tare da kiran a basu kula da alhazansu, idan har za a bi tsari hakan ba matsala ba ne."
- Muhmmad Abdullahi
Abba ya ba mahajjata riyal 100
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Abba Kabir ya ba mahajjatan jihar Kano 3,121 goron sallah a kasar Saudiyya.
Abba ya ba kowane mahajjaci riyal 100 domin gudanar da Sallah cikin walwala yayin da suke kasa mai tsarki domin aikin hajji.
Asali: Legit.ng