Bankin Duniya Ya Ci Gyaran Tinubu da CBN, Ya Gargadi Gwamnati Kan Hauhawar Farashi

Bankin Duniya Ya Ci Gyaran Tinubu da CBN, Ya Gargadi Gwamnati Kan Hauhawar Farashi

  • Bankin Duniya ya tura gargadi ga gwamnatin Najeriya kan daukan matakai masu tsauri da niyyar farfaɗo da tattalin arzikin kasar
  • Bankin ya ce ɗaukan tsauraran matakai kamar karin kudin ruwa a lokutan ba al'umma bashi ba zai kawo saukin rayuwa ba a kasar
  • Cikin rahoton da bankin ya fitar ya yi hasashen yadda haɓakar tattalin arzikin Najeriya zai kasance cikin shekarun 2024 da 2025

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Nigeria - Bankin Duniya ya gargadi gwamnatin Najeriya kan karin kudin ruwa ga masu karbar bashin bankuna.

Bankin ya fitar da gargadin ne biyo bayan karin kudin ruwa da bankin CBN ya yi ga masu karɓar bashi a bankuna.

Kara karanta wannan

Magana ta ƙare, Bankin Duniya ya ba Najeriya bashin $2.2bn, ministan Tinubu ya magantu

Bola Tinubu
Bankin Duniya ya bukaci a rage kudin ruwa a Najeriya. Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Dankin Duniya ya fitar da bayanin ne cikin wani rahoton da ya fitar a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Karin kudin ruwa a Najeriya

Cikin rahoton da bankin ya fitar ya nuna cewa an samu karin kudin ruwa a Najeriya da kashi 3.75% daga watan Fabrairu zuwa Mayu.

Bankin ya ce a watan Fabrairu kudin ruwa yana kashi 22.75% amma zuwa watan Mayu ya karu zuwa kashi 26.25%.

Karin kudin ruwa zai kawo cigaba?

Bankin Duniya ya ce karin kudin ruwan ba zai haifar da ɗa mai ido ga Najeriya da al'ummarta ba musamman wajen rage tashin farashi.

A cewar bankin, idan aka samu karin kudin ruwa, masu sana'o'i da dama za su rasa damar karbar bashi a bankuna kuma hakan zai kara matsin rayuwa a kasar.

Tattalin Najeriya a 2024 da 2025

Kara karanta wannan

Bankin CBN ya soke lasisin wasu manyan bankuna 4 a Najeriya? Gaskiya ta fito

Cikin rahoton da bankin ya fitar yayi hasashen rashin haɓakar tattalin Najeriya a karshen 2024 zuwa 2025, rahoton the Cable.

Bankin ya ce tattalin zai iya kasancewa a kan kashi 3.3% a 2024 sannan zai dawo 3.5% a 2025 wanda ba wani bambanci bane a mahangar masana.

Saboda haka bankin ya yi kira ga gwamnatin Najeriya kan kaucewa karin kudin ruwa da nufin kawo karshen tashin farashin kayayyaki ko kuma habaka tattalin arziki.

Bankin Duniya ya ba Najeriya bashi

A wani rahoton, kun ji cewa Bankin Duniya ya amince ya ba Najeriya jimillar bashin $2.25bn domin sake fasali da daidaita tattalin arzikin kasar.

Ana hasashen cewa wannan bashin na $2.25bn zai taimakawa kokarin Najeriya na dawo da tattalin arziki da tallafawa talakawan kasar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng