InnalilLahi: An Shiga Ɗimuwa Bayan Ƙarin Rasuwar Mahajjatan Najeriya 2 Nan Take a Makkah

InnalilLahi: An Shiga Ɗimuwa Bayan Ƙarin Rasuwar Mahajjatan Najeriya 2 Nan Take a Makkah

  • Mutane sun shiga tashin hankali bayan samun karin rasuwar mahajjata biyu daga jihar kwara da ke Arewacin Najeriya
  • Mahajjatan da aka bayyana da Salman Muhammad Alade da Ayishat Shuaib Ologele sun rasa ransu ne bayan fama da gajeruwar rashin lafiya
  • Hukumar alhazan jihar Kwara ta tura sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasu tare da yi musu addu'ar samun rahama

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Makkah, Saudiyya - An samu rasuwar karin mahajjata guda biyu a kasar Saudiyya yayin aikin hajji.

Mahajjatan guda biyu sun fito ne daga jihar Kwara da aka bayyana da Salman Muhammad Alade da kuma Ayishat Shuaib Ologele.

Karin mahajjata 2 daga Najeriya sun rasu a Makka
Wasu mahajjata 2 daga jihar Kwara a Najeriya sun rasu a Makkah yayin aikin hajji. Hoto: Inside Haramain.
Asali: Facebook

Hajji: Yawan wadanda suka rasu daga Kwara

Kara karanta wannan

Saudiyya ta fadi adadin mahajjatan bana, ta fadi damuwa 1 da za a fuskanta

Daily Trust ta tattaro cewa mutuwar mahajjatan guda biyu ya tabbatar da rasa akalla mutane hudu kenan daga jihar Kwara.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An tabbatar cewa Ayishat Shuaib Ologele ta rasa ranta ne yayin tafiya daga Makkah zuwa Madinah.

Yayin da Salman Muhammad Alade shi ma ya fara rashin lafiyar a Makkah inda ya ce ga garinku nan take.

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto hukumomi ba su tabbatar da musabbabin mutuwar mahajjatan ba.

Sai dai hukumar alhazan jihar Kwara ta jajantawa iyalan wadanda suka rasu inda ta yi addu'ar samun rahama a gare su.

Kwara: Hukumar NAHCON ta yi martani

Babban sakataren hukumar a jihar, Abdulsalam Abdulkadir shi ya tabbatar da haka a yau Alhamis 13 ga watan Yuni.

"Tabbas mun yi rashin mahajjata 2 daga jihar Kwara, za mu yi magana daga baya yanzu ina cikin ganawa."

Kara karanta wannan

"Duk da masu ja da ikon Allah, mun yiwa mutanen Kano aiki," Gwamna Abba gida gida

"Mun tura sakon ta'aziyya ga iyalan wadanda suka rasu, muna musu addu'ar Ubangiji ya yafe musu kura-kuransu."

- Abdulsalam Abdulkadir

Wata Hajiya ta hallaka kanta a Makkah

A wani labarin, kun ji cewa ana fargabar wata Hajiya mai suna Hawawu ta hallaka kanta a birnin Madina da ke kasar Saudiyya.

Hajiyar ta fito ne daga jihar Kwara inda hukumomin Saudiyya suka tabbatar da haka bayan gudanar da bincike.

Hukumomin sun sanar da hukumar alhazai ta jihar Kwara yadda al'amarin ya faru a Madina bayan samun gawar matar.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel