Saudiyya Ta Fadi Adadin Mahajjatan Bana, Ta Fadi Damuwa 1 da Za a Fuskanta

Saudiyya Ta Fadi Adadin Mahajjatan Bana, Ta Fadi Damuwa 1 da Za a Fuskanta

  • Kasar Saudiyya ta ambaci adadin mahajjatan da za su gabatar da aikin Hajjin shekarar 2024 yayin da shirye-shirye suka kammala
  • Jami'in yada labaran ma'aikatar lafiya ta kasar ya ambaci babbar matsalar da mahajjata za su iya fuskanta yayin Hajjin bana
  • Sai dai duk da hasashen, jami'in ya bayyana matakin da kasar ta dauka domin ganin komai ya tafi lafiya a lokacin aikin Hajjin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Saudi Arabia - Kasar Saudiyya ta yi karin haske kan adadin mahajjatan da suka iso kasar daga dukkan fadin duniya.

Saudiyya ta fadi haka ne yayin da ake kokarin fara aikin Hajjin shekarar 2024 a gobe Juma'a, 14 ga watan Yuni.

Kara karanta wannan

"Duk da masu ja da ikon Allah, mun yiwa mutanen Kano aiki," Gwamna Abba gida gida

Kasar Saudiyya
Saudiyya ta ce mahajjata 1,547,925 ne za suyi aikin Hajji a bana. Hoto: Inside the Haramain
Asali: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa jami'in sadarwa na ma'aikatar lafiyar kasar ya shawarci mahajjata kan zafi da ake a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Adadin mahajjatan bana a Saudiyya

Jami'in ma'aikatar samar da fasfo a kasar Saudiyya ya bayyana cewa a bana an samu adadin mutane 1,547,925 da suka iso kasar domin aikin Hajji.

Jami'in ya ce wannan shi ne adadin mutanen da suka zo kasar ta tashar jiragen sama, motoci da kuma tashar jiragen ruwa, rahoton Daily Sun.

Matsalar zafi a Saudiyya

Jami'in yada labaran ma'aikatar lafiyar kasar Saudiyya, Dr. Muhammad Al-Abdullaali ya ce babbar matsalar da za a fuskanta a bana itace zafi.

Muhammad Al-Abdullaali ya ce an samu karin zafi a kasar yayin da aikin Hajjin bana ke kokarin kankama.

Zafi: Matakin da Saudiyya ta ɗauka

Muhammad Al-Abdullaali ya bayyana cewa kasar tanadi lemar hannu, ruwan sha da inuwa da za a rika hutawa.

Kara karanta wannan

Rundunar sojin Najeriya ta dauki matakin gaggawa kan cin zarafin farar hula a Legas

Saboda haka ya shawarci mahajjatan da su rika bin dokokin da hukumar lafiya ta gindaya domin kammala aikin Hajji cikin sauki.

An kara tsaro a Saudiyya

A wani rahoton, kun ji cewa jami'an tsaron kasar Saudiyya sun yi atisaye domin nuna shirin ba da kariya ga dukkan mahajjatan shekarar 2024.

Hukumomin kasar sun tabbatar da ɗaukan sababbin matakan kara tsaro a wurare da dama ciki har da asibitoci da wuraren karbar magani da dama.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng