Babbar Sallah: An Sanar da Ganin Watan Dhul Hijjah a Saudiyya, Bayanai Sun Fito

Babbar Sallah: An Sanar da Ganin Watan Dhul Hijjah a Saudiyya, Bayanai Sun Fito

  • Hukumomi a kasar Saudiyya sun sanar da ganin watan Dhul Hijjah a yammacin yau Alhamis 6 ga watan Yuni
  • Sanarwar ta tabbatar da cewa gobe Juma'a 7 ga watan Yuni zai kasance 1 ga watan Dhul Hijjah na shekarar 1445
  • Za a yi Arfa a ranar Asabar 15 ga watan Yuni sai kuma babbar sallah a ranar Lahadi 16 ga watan Yunin wanna shekara

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Riyadh, Saudiyya - Hukumomi a kasar Saudiyya sun tabbatar da ganin wata da yammacin yau Alhamis 6 ga watan Yuni.

An sanar da ganin watan Dhul Hijjah na shekarar 1445 ne a ƙasar wanda hakan ya tabbatar da gobe ne 1 ga wata.

Kara karanta wannan

Hadari: 'Dan takarar 2023, Obi ya ziyarci tauraron S/Eagles, Tijjani Babangida yana jinya

Sa'udiyya ta sanar da ganin watan Dhul Hijjah
An sanar da ganin watan Dhul Hijjah a Saudiyya. Hoto: @insharifain.
Asali: Facebook

Saudiya ta ga watan Dhul Hijjah

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Inside the Haramain ta wallafa a shanfinta na X a yau Alhamis 6 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta tabbatar da cewa gobe Juma'a 7 ga watan Yuni zai kasance 1 ga watan Dhul Hijjah 1445.

Hari ila yau, za a yi Arfa a ranar Asabar 15 ga watan Yuni yayin da za a gudanar da babbar Sallah ranar Lahadi 16 ga watan Yuni.

Yawan maniyyata da suka isa Saudiyya

Wannan na zuwa ne yayin ake shirye-shiryen gudanar da aikin hajjin bana da ake yi a watan Dhul Hijjah a kasar.

Hukumomi a kasar Saudiyya sun bayyana cewa kimanin maniyyata ‘yan kasashen waje miliyan daya ne suka isa aikin hajjin 2024.

Akalla musulmai miliyan biyu ne ake sa ran za su yi aikin hajjin bana a Makkah inda ake tsammanin 65,000 za su fito daga Najeriya.

Kara karanta wannan

Minista ya mika mafi karancin albashin N105,000 ga Tinubu? an fayyace gaskiya

Saudiyya ta fara duban watan Dhul Hijjah

Kun ji cewa hukumomi a ƙasar Saudiyya sun buƙaci al'ummar musulmi na ƙasar su fara duba jinjirin watan Dhul Hijjah gobe Alhamis.

Watan Dhul Hijja wanda ya kasance wata na 12 a jerin watannin addinin Musulunci, shi ne watan da Musulman duniya ke yin sallar Layya.

Ranar Alhamis 6 ga watan Yunin 2024 za ta kasance dai-dai da 29 ga watan Dhul Qa'ada, bisa haka hukumomin Saudiyya suka nemi a fara duban watan 12.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.