"Yadda 'Yan Bindiga Suka Yi Ta'adi a Jeji, Haka El Rufai Yayi a Ofis a Kaduna", Sanata

"Yadda 'Yan Bindiga Suka Yi Ta'adi a Jeji, Haka El Rufai Yayi a Ofis a Kaduna", Sanata

  • Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya yaba da yadda majalisar jiharsa suka gano badakala a gwamnatin da ta shude
  • 'Yan majalisar sun yi zargin gwamnatin Nasir El Rufa'i ta yi almundahanar kudade N423bn lokacin ludayinsa yana kan dawo, inda aka kafa kwamitin bincike
  • Sanata Shehu Sani ya ce ta'addanci biyu aka yi a jihar, na daji da na gidan gwamnati, kuma yanzu abin da ya rage shi ne su ƙwato hakkin mutanen Kaduna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Kaduna- Tsohon Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya yaba da yadda 'yan majalisar jiharsa suka jajirce wajen bankado zargin badakala a tsohuwar gwamnatin Nasir El Rufa'i. 'Yan majalisar na zargin Nasir El Rufa'i da almundahanar kudin gwamnati tare da wasu 'yan kwangila ne suke 'sace' kudin al'umma.

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar ya bankaɗo 'dalilin' ɓoye ɓoyen gwamanti kan tallafin fetur

Shehu Sani
Sanata Shehu Sani ya bukaci 'yan majalisar Kaduna ta ci gaba da binciken Nasir El Rufa'i Hoto: Shehu Sani, Nasir El-Rufa'i
Asali: Facebook

Gwamnatin Uba Sani na zargin tsohon Gwamnan wanda suke jam'iyya daya da almundahanar N423bn, inda Shehu Sani ya ga dacewar bibiyar batun kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X.

'A kwato kudin daga hannun El Rufa'i,' Sani

Jaridar Leadership News ta wallafa cewa tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Shehu Sani ya nemi 'yan majalisa su bi doka wajen kwato kudin da ake zargin Nasir El Rufa'i ya wawushe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya yi zargin tsohon gwamna Nasir El Rufa'i ya tarawa yaransa dukiya amma ya bar talakawan Kaduna cikin bashi dumu-dumu.

Shehu Sani ya ce ta'addanci biyu mutanen jiharsa suka fuskanta, da na daji da na gidan gwamnati.

Ya shawarci 'yan majalisar su gaggauta kwato hakkin talakawan jihar daga hannun tsohon gwamnansu.

'Kan ku ake ji," Nasir El Rufa'i

Kara karanta wannan

'A rage ciki', An bukaci 'yan majalisa su rage albashinsu domin a samu kudi

A baya mun kawo muku labarin cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna Nasir El Rufa'i ya ce bincikensa da gwamnatin Uba Sani take yi sharrin siyasa ne kawai.

Mai magana da yawun tsohon gwamnan, Muyiwa Adekeye ya ce mai gidansa ya yi mulkin jiharsa cikin adalci da tsafta.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Online view pixel