Hajj 2024: Adadin Alhazan da Suka Isa Saudiya Zuwa Yanzu Ya Kai Miliyan 1

Hajj 2024: Adadin Alhazan da Suka Isa Saudiya Zuwa Yanzu Ya Kai Miliyan 1

  • Kimanin alhazan kasashen waje miliyan daya ne suka isa kasar Saudiya domin gudanar da aikin hajjin shekarar 1445
  • A ranar Lahadin da ta gabata, jimillar maniyyata 935,966 ne suka isa Saudiya ta tashoshin jiragen ruwa, sama da tituna
  • Akalla musulmai miliyan biyu ne ake sa ran za su je aikin hajjin bana a Makkah inda ake sa tsammanin 65,000 daga Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kasar Saudiya - Hukumomi a kasar Saudiyya sun bayyana cewa kimanin maniyyata ‘yan kasashen waje miliyan daya ne suka isa aikin hajjin shekarar 2024.

Maniyyata miliyan 1 sun isa Saudiya
Hajj 2024: Alhazai miliyan 1 sun isa Saudiya zuwa ranar Asabar. Hoto: @MoHU_En
Asali: Facebook

Mutane miliyan 1 sun isa Saudiya

Ya zuwa karshen ranar Lahadin da ta gabata, adadin maniyyata 935,966 ne suka isa Saudiya ta tashoshin jiragen ruwa da jiragen sama da kuma tituna.

Kara karanta wannan

Rahoto: Yajin aikin 'yan ƙwadago ya jawo Najeriya ta yi asarar Naira biliyan 149

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Rahoton da Saudi Gazette ta fitar ya nuna cewa mafi yawan mahajjata sun shiga Saudiya ta jirgin sama wanda adadinsu ya kai 896,287.

Haka zalika, adadin maniyyatan da suka isa kasar ta tituna ya kai 37,280, yayin da mahajjata 2,399 suka shiga Saudiya ta tashoshin ruwa.

Saudiya ta kirkiri kwagirin Nusuk

Rahotanni sun ce sama da musulmai miliyan biyu ne ake sa ran za su halarci aikin hajjin shekara 2024 a Makkah inda ake sa tsammanin ‘yan Najeriya 65,000 za su yi aikin.

Tuni dai hukumar alhazai ta kasa (NAHCON) ta ce ta yi jigilar alhazan Najeriya 40,696 zuwa Saudiya daga cikin jimillar jirage 96 kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Har ila yau, ministan Hajji da Umrah na kasar Saudiya, Dr Tawfiq Al-Rabiah, ya kaddamar da kwagirin Nusuk na intanet, irinsa na farko a duniya domin hidimtawa alhazan Hajji da Umrah.

Kara karanta wannan

Kasar Saudiyya ta dauki tsauraran matakai kan masu zuwa hajji ta barauniyar hanya

Saudiya ta gargadi marasa katin Nusuk

A wani labarin, mun ruwaito cewa hukumomin Saudiya sun sanar da cin tarar SR10,000 (kimanin N3,991,170) ga maniyyatan da aka kama ba tare da katin shaida na NUSUK ba.

NUSUK wani katin shaida ne da ma’aikatar Hajji da Umrah ta Saudiyya ta bullo da shi domin saukaka zirga-zirgar dukkanin alhazai a wurare masu tsarki a aikin Hajjin shekarar 2024.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.