Gobarar Titi a Jos: Attajiri Zai Biya Tsohuwar Matarsa Naira Tiriliyan 1.3 Saboda Sun Rabu
- Wata kotu a Koriya ta Kudu ta umarci shugaban rukunin kamfanonin SK Chey Tae-won da biyan daloli ga tsohuwar matarsa
- An umarci Chey Tae-won ya biya tsohuwar matarsa Roh So-yoeng kuma diyar tsohon shugaban kasar $1bn saboda azabtar da zuciyarta
- Chey Tae-won ya rabu da matarsa ne bayan an gano ya ajiye sa-daka a gefe har sun haihu tare, wanda dalilin haka ne auren ya mutu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. South Korea- Wata kotu da ke zamanta a Koriya ta kudu ta umarci shugaban rukunin kamfanonin SK, Chey Tae-won ya biya tsohuwar matarsa Roh So-young won tiriliyan 1.38, wanda ya zo daidai da $1bn.
Shugaban SK ya rabu da Roh So-young, diyar tsohon shugaban kasar bayan an gano yana da sa-daka, kuma har sun haihu tare.
BBC News ta ruwaito wannan kudi shi ne mafi yawa da aka taba bayarwa a tarihin mutuwar aure a kasar.
Dalilin zuwa Roh So-young kotu
Diyar tsohon shugaban kasar Koriya ta kudu, Roh So-young ta maka mijinta kotu bisa zargin cin amana. Ta shaidawa kotu cewa ajiye budurwa da mijinta ya yi ya jefa ta cikin mummunan yanayi, inda ta nemi a bata kaso mai tsoka na dukiyarsa, kamar yadda Bangkok Post ta wallafa. Da take yanke hukunci, kotun ta umarci shahararren mai kudin, Chey Tae-won ya biya tsohuwar matarsa S1bn. Kotun ta kuma mallaka mata hannun jari na kamfanin, ganin cewa tayi amfani da alakar mahaifinta wajen cicciba kamfanonin SK.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Chey Tae-won zai daukaka kara
Kudin da kotu ta nemi Chey Tae-won ya ba tsohuwar matarsa kari ne kan won biliyan 66.5 da wata karamar kotu ta umarci ya biya a shekarar 2022. Yanzu haka lauyoyin hamshakin dan kasuwar sun ce za su daukaka kara, ganin yadda Roh So-young ke amfaninsa sanayyya rana dakile cinikayyar kamfanonin su.
An hana sayar da tufafin shugaban Koriya
A baya mun kawo muku labarin cewa shugaban kasar Koriya ta Arewa, Kim Jung-un ya haramtawa shaguna a kasar sayar da irin tufafin da yake sawa.
Haka kuma shugaban ya hana sayar da rigar sanyin fatar dabbobi da irin tufafin da yake sawa saboda ya zama shi kadai ke da su a fadin kasar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng