Al Maktoum: Dubai Za Ta Gina Tashar Jirgin Sama Mafi Girma a Duniya
- Domin zama lamba daya a harkar sufurin jiragen sama a duniya, Dubai za ta gina sabuwar tashar jiragen sama ta Al Maktoum
- Idan aka kammala ginin, filin jiragen sama na Al Maktoum zai zama mafi girma a duniya kuma mafi tsada wajen ginawa
- Mai mulkin ƙasar Dubai, Sheikh Mohammed bin Rashid al-Maktoum ya amince da kashe AED biliyan 128 (N43trn) wajen gina tashar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
UAE, Dubai - Mai mulkin ƙasar Dubai, Sheikh Mohammed bin Rashid al-Maktoum ya amince da gina sabuwar tashar fasinjoji a filin jiragen sama na Al Maktoum.
Filin jirgi mafi girma a duniya
Kamar yadda ya sanar a shafinsa na Twitter a ranar Lahadi, Sheikh Rashid al-Maktoum, ya ce tashar za ta lakume AED biliyan 128 (N43trn).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Filin jiragen sama na Al Maktoum zai zama mafi girma a duniya yayin da zai iya daukar fasinja sama da miliyan 260 a lokaci daya.
Mai mulkin ƙasar ya ce filin jirgin Al Maktoum zai nunka girman filin jirgin Dubai sau biyar, wanda zai sa a mayar da ayyukan filin zuwa Al Maktoum a shekaru masu zuwa.
Dubai za ta zama lamba daya?
An ruwaito cewa za a samar da kofofin shiga tashar jirgi guda 400 a cikin filin jirgin Al Maktoum yayin da za a gina hanyoyin jirgi guda biyar.
Wannan sabon filin jiragen zai kasance gida ga kamfanin jiragen Emirates na kasar Dubai da takwararsa ta Flydubai da sauran jiragen da ke jigila a Dubai.
Sheikh Rashid al-Maktoum, ya ce wannan matakin zai jaddada matsayin Dubai na zama lamba daya a harkar sufurin jiragen sama a duniya.
Matakin farko na gina tashar jirgin
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Sheikh Ahmed bin Saeed Al Maktoum, shugaban kamfanin Emirates ya ce:
"Za a fara kashi na farko na aikin da kammala shi a cikin shekara 10, inda za a iya fara jigilar akalla fasinjoji miliyan 150 a lokaci daya."
Mahukunta na so tashar jirgin Al Maktoum idan an kammala ta maye gurbin tashar jirgin Dubai wacce ke jigilar fasinja miliyan 120 a shekara.
Me ya jawo ambaliyar ruwa a Dubai?
A wani rahoton, Legit Hausa ta yi nazari kan ikirarin ma'abota amfani da shafukan sada zumunta na cewa amfani da fasahar 'cloud seeding' ne ya jawo ambaliyar ruwa a Dubai.
Duk da cewa fasahar kirkirar gajimare kan iya zubar da ruwa mai yawan da zai iya jawo ambaliya, sai dai bincike ya nuna babu alakar ambaliyar ruwa a Dubai da fasahar 'cloud seeding.'
Asali: Legit.ng