Daga karshe, an bude babban filin jirgin saman Abuja

Daga karshe, an bude babban filin jirgin saman Abuja

Hukumar jiragen saman Najeriya FAAN ta sanar da cewa an bude babban filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe International Airport, Abuja, bayan wani jirgi da ake zargin na tsoho gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sherrif ne.

Wani jawabin da Manajan hukumar FAAN , Mrs Henrietta Yakubu, ta saki yau Alhamis, ta bayyana cewa jirgin ya fita daga kan hanya yayinda take kokarin sauka kuma ta makale a kan hanya.

Henrietta Yakubu ta bayyana cewa an bude filin jirgin domin sufuri bayan rage titin gudu zuwa mita 3000.

Daga karshe, an bude babban filin jirgin saman Abuja
Daga karshe, an bude babban filin jirgin saman Abuja
Asali: Facebook

Ta bada tabbacin cewa jirage da fasinjoji su koma sufuri kamar yadda ya kamata.

Legit.ng ta kawo muku rahoton cewa An kulle babban filin jirgin saman Nnamdi Azikwe International Airport, da ke birnin tarayya Abuja bayan wata jirgin sama ta toshe hanyar wucewab jirgi.

Wanna abu ya faru ne misalin karfe 10 na daren jiya Laraba. Majiya mai karfi sun bayyanawa jaridar Daily Nigerian cewa jirgin kira 5N BOD Gulfstream na tsohon gwamnan jihar Borno, Ali Modu Sheriff ne.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel