"Mun Gano Inda Ya Ke", Gwamnati Ta Yi Karin Haske Kan Shugaban Binance da Ya Tsere

"Mun Gano Inda Ya Ke", Gwamnati Ta Yi Karin Haske Kan Shugaban Binance da Ya Tsere

  • Bayan shugaban Binance, Nadeem Anjarwalla ya tsere daga Najeriya, gwamnatin Tarayya ta zakulo inda ya ke
  • Gwamnatin ta tabbatar da cewa an samu Anjarwalla ne a kasar Kenya bayan ya tsere daga kulle a Najeriya a kwanakin baya
  • Fadar shugaban kasa ta tabbatar da cewa ta haɗa kai da sauran hukumomin tsaro da 'yan sandan Kenya domin dawo da shi Najeriya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ta gano inda shugaban Binance da ya tsere, Nadeem Anjarwalla ya ke.

Gwamnatin ta ce ta gano Anjarwalla ya na kasar Kenya bayan tserewar shugaban Binance daga kulle Najeriya a kwanakin baya.

Kara karanta wannan

Watanni 2 da maganar komawa APC, Abba ya dauko binciken Ganduje da iyalinsa

Gwamnatin Tarayya ta gano inda shugaban Binance, Anjarwalla ya tsere
Gwamnatin Tarayya ta gano shugaban Binance, Nadeem Anjarwalla a Kenya bayan ya tsere daga Najeriya. Hoto: @kc_journalist.
Asali: Twitter

Wane mataki EFCC, 'yan sanda suka dauka?

Dalilin haka ne ma ya sa hukumar EFCC da rundunar 'yan sandan Najeriya da na Kenya suka fara tattaunawa kan yadda za a dawo dashi Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Punch ta tattaro cewa Anjarwalla bayan tserewarsa ya gudu ne kasar Kenya domin gujewa hukunci.

Wata majiya daga fadar shugaban kasa ta tabbatar da haka inda ta ce ana ƙoƙarin dawo da shi Najeriya, cewar BusinessDay.

Yadda ake gano Anjarwalla a Kenya

"Mun same shi, mun san inda ya ke, ya na kasar Kenya, muna aiki da wasu hukumomi domin tabbatar da cewa ya dawo Najeriya."

- Cewar majiyar

Hukumomin tsaro a Najeriya da rundunar 'yan sandan kasa da kasa sun hada kai da 'yan sandan Kenya domin dawo dashi Najeriya ya fuskanci hukunci.

Hukumar EFCC na zargin Anjarwalla kan wasu laifuffuka biyar da suka shafi rashin biyan haraji da badakalar kudi kimanin $35.4m da sauransu.

Kara karanta wannan

Ministan tsaro ya caccaki dattawan Arewa kan kalaman da suka yi game da Bola Tinubu

Daya daga cikin abokan aikin Anjarwalla, Tigran Gambaryan ya na hannun jami'an EFCC tun a kwanakin baya, cewar rahoton Daily Post.

Anjarwalla ya tsere daga kulle

A baya, mun kawo muku labarin cewa shugaban Binance, Nadeem Anjarwalla ya tsere daga kulle da ake masa a birnin Tarayya Abuja.

Ana zargin Anjarwalla da saba dokokin kasa da suka hada da rashin biyan haraji da sauran laifuffuka.

Daga bisani, mai ba Shugaba Tinubu shawara kan harkokin tsaro, Nuhu Ribadu ya ce sun dauki mataki kan wadanda tsaron Anjarwalla ke hannunsu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.