Jerin Kasashen Duniya 6 Inda Rana Ba Ta Faduwa, Ga Cikakken Bayani
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Rayuwarmu ta yau da kullun na wakana ne a sa'o'i 24 a kowacce rana. Yayin da kusan awanni 12 na kasancewa lokacin yini, sauran sa'o'in kuma na kasancewa lokacin dare. Amma, ko ka san cewa akwai kasashen duniya da rana ba ta faɗuwa sama da kwanaki 70?
A wasu sassa na duniya kamar Norway, Kanada, Iceland, da Finland, wani lamari mai ban sha'awa yana faruwa inda rana ke zuwa kusa da Da'irar Arctic, The Nation ta ruwaito.
Wannan abin da ke faruwa 'na musamman' yana haifar da nau'ikan hasken rana da duhu, yana daidaita salon rayuwa da ayyukan mazauna garuruwan.
Time of India ta jero bayanin wasu kasashe shida da rana ba ta faɗuwa, da ya kamata ku sani:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Norway
Ƙasar tana cikin yankin Da'irar Arctic kuma ta amsa sunanta na "Kasar da rana ke fitowa lokacin dare" inda rana ta ke fitowa daga Mayu zuwa karshen Yuli ba tare da faɗuwa ba, tsawon kwanaki 76.
A Svalbard, Norway, rana tana haskakawa ba tare da dusashewa ba daga 10 ga Afrilu zuwa 23 ga Agusta, wanda ya mai da ita yankin arewacin Turai da mutane suka fi zama.
Nunavut, Kanada
Garin na da tazarar digiri biyu sama da Da'irar Arctic, a cikin yankunan Arewa maso Yamma na Kanada, yankin yana fuskantar kusan watanni biyu na hasken rana ba tare da ta fadi ba.
Iceland
Kasar ta kasance a cikin Turai kuma sananna ce saboda kasancewarta tsibiri na biyu mafi girma a nahiyar bayan na Burtaniya.
Iceland ta yi fice saboda rashin sauro. A lokacin bazara, rana kan fito a cikin dare kuma ta yi haske, ba ta faɗuwa cikin watan Yuni.
Barrow, Alaska
A cikin wannan yanki, rana na kasancewa a saman sararin samaniya daga karshen Mayu zuwa karshen Yuli, wanda ke haifar da ci gaba da hasken rana ko da dare ya yi.
Sabanin haka, daga farkon watan Nuwamba, rana ba ta fitowa tsawon kwanaki 30 a jere, wanda ke nuna farkon daren 'polar'.
Sweden
Ƙasar tana samun tsayuwar hasken rana har na tsawon watanni shida a shekara.
Daga farkon watan Mayu har zuwa karshen watan Agusta, rana na faduwa da tsakar dare sai ta sake fitowa da karfe 4 na asuba.
Finland
A lokacin bazara, yankuna da yawa na Finland suna shafe kwanaki 73 a jere ba tare da faɗuwar rana ba, amma a cikin hunturu, yankin ba shi da hasken rana.
Sakamakon haka, mazauna garin na daidaita yanayin barcinsu, suna yin barci sosai a lokacin hunturu saboda dogon dare da kuma rage barci a lokacin rani saboda dadewar hasken rana.
Gwamnati ta kaddamar da kwamitin karin albashi
A wani labarin, mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya kaddamar da wani kwamitin mutum 36 da zai yi aikin kara albashi ga ma'aikata.
Kwamitin zai yi dogon nazari tare da ba gwamnati shawara kan mafi ƙarancin albashin da ya kamata ma'aikatan kasar su rinka dauka.
Asali: Legit.ng