Ƙaramin yaro ya ƙera fitila mai amfani da hasken rana

Ƙaramin yaro ya ƙera fitila mai amfani da hasken rana

Wani karamin yaro dan kasar Kenya mai shekaru 11 ya baiwa jama’a da dama mamaki da irin basirar da Allah yayi mai.

Ƙaramin yaro ya ƙera fitila mai amfani da hasken rana

Wannan yaro da ba’a bayyana sunansa ba ya kera wata na’urar haske daga robobin Blue Band mai amfani da hasken rana. Basirar wannan yaron ta sanya shi yayi suna a kafafen sadarwa, inda jama’a suka dinga tattauna batun sa, da hikimarsa.

Sa’annan duk a cikin na’aurar, ya sanya man bota da ake cin buredi dashi ya zamto wani sinadarin da za’a iya cajin waya da shi, tare da samar dab akin da za’a jona wayar, duk a jikin roban Blue Band.

Ƙaramin yaro ya ƙera fitila mai amfani da hasken rana

KU KARANTA: Yara na komawa makaranta a Borno

A yanzu dai da na’aurar yaron ake amfani a gidansu don hasakaka da dare, har ma makwabtansu na amfani da na’urar.

Ƙaramin yaro ya ƙera fitila mai amfani da hasken rana

Yaron yace ya tattaro robobin Blue Band ne dayawa daga bola, sa’annan ya samo faifan na’aurar sola lalatattu, inda ya gyara su, da haka ne ya samar da nasa na’urar wanda yake yi masa caji da rana, sai yayi amfani da shi da dare.

Fatan mu anan, shine a taimaka ma yaron.

Za'a iya bin kadin labaran mu a shafin Tuwita @naijcomhausa

&feature=youtu.be

Asali: Legit.ng

Online view pixel