Burtaniya Ta Dauki Mataki Kan Mambar Majalisa 'Yar Najeriya Saboda Kalaman Goyon Bayan Gaza

Burtaniya Ta Dauki Mataki Kan Mambar Majalisa 'Yar Najeriya Saboda Kalaman Goyon Bayan Gaza

  • 'Yar Majalisa a Burtaniya ta hadu da fushin hukumomi bayan dakatar da ita daga Majalisar bayan kalamanta kan Gaza
  • Kate Osamor wacce 'yar Najeriya ce ta yi kalaman ne a ranar Lahadi 28 ga watan Janairu ana shirin bikin tunawa da kisan Yahudawa miliyan shida
  • Kate ta kwatanta kisan gillar da Isra'ila ke yi kan Gaza da wanda aka yi kan Yahudawa da ya yi ajalin mutane miliyan shida

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Landan, Burtaniya - Jami'yyar LP ta dakatar 'yar Majalisa kan kalamanta da ya shafi kisan gilla da Isra'ila ke yi.

'Yar Majalisar, Osamor Kate wacce asali 'yar Najeriya ce ta bayyana ra'ayinta ne kan kisan da Isra'ila ke aikatawa kan Gaza.

Kara karanta wannan

A karshe, rundunar sojin saman Najeriya ta nemi afuwar mutane kan kuskuren kashe bayin Allah a arewa

Burtaniya ta dakatar da 'yar Najeriya a Majalisa kan kalamai game da Gaza
Burtaniya ta dakatar da 'yar Najeriya a Majalisar kasar. Hoto: Kate Osamor.
Asali: Twitter

Wane mataki aka dauka kan Kate?

Kate ta kwatanta kisan gillar da Isra'ila ke yi kan Gaza da wanda aka yi kan Yahudawa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tuni Kate da ke wakiltar Edmonton ta ba da hakuri kan kalamanta da ta yi a ranar Lahadi 28 ga watan Janairu.

Har ila yau, Yahudawa sun yi Allah wadai da kalaman Kate wanda ta yi misali da su.

Mai ladabtarwa a Majalisar ya dakatar da ita tare da kaddamar da bincike kan lamarin don daukar mataki.

Daily Trust ta tattaro cewa Kate ta bayyana haka ne yayin bikin tunawa da kisan Yahudawa da sauran wadanda aka ci zarafi a duniya.

Mene Kate ta rubuta kan Gaza?

Rahotanni sun tabbatar da cewa ana bikin Holocaust Memorial Day (HMD) don nuna alhini kan kisan Yahudawa miliyan shida a duniya.

Kara karanta wannan

Siyasar jihar PDP ta sake rikicewa bayan hadimar gwamnan ta ajiye mukaminta, akwai dalilai masu yawa

Kate ta rubuta a shafinta na X kamar haka:

"Gobe ne ranar tunawa da kisan Yahudawa miliyan shida a duniya da sauran mutane karkashin jagorancin Nazi.
"Sai kuma kisan gillar baya-bayan nan da aka yi a Cambodia da Rwanda da Bosnia da kuma abin da ya faru yanzu a Gaza."

Fasto ya gargadi malamai kan Isra'ila

A wani labarin, Fitaccen Fasto a Najeriya ya gargadi takwarorinsa Fastoci kan yi wa Isra'ila addu'o'i a Najeriya.

Faston ya ce bai kamata su na da bukatar addu'a a Najeriya sannan su je su na yi Isra'ila addu'a ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.