Mun Gaji: Ba Za Mu Lamunci Sace Mana ‘Ya’ya da Sayar Da Su Ba, Sarkin Kano Ya Fusata
- Sarkin Kano, Mai Martaba Aminu Ado Bayero ya tura zazzafan gargadi kan masu garkuwa da yara a jihar
- Sarkin ya ce ba za su lamunci satar yara da kuma siyar da su ba zuwa yankin Kudancin Najeriya
- Sarkin ya bayyana haka ne a yau Asabar 6 ga watan Janairu a Kano yayin ganawa da manema labarai
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Mai Martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya yi Allah wadai da sace-sacen yara kanana daga Arewa zuwa Kudancin kasar.
Bayero ya kuma nuna damuwa kan yadda yin garkuwa da mutane ya zama ruwan dare musamman a Arewacin Najeriya.
Mene Ado Bayero ke cewa a Kano?
Daily Nigerian ta tattaro cewa Sarkin ya bayyana haka ne a yau Asabar 6 ga watan Janairu a Kano yayin ganawa da manema labarai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sarkin, wanda ya samu wakilci Dan Malikin Kano, Ahmad Umar ya ce masarautar ba za ta zuba ido ana dibar yara zuwa Kudancin kasar ba.
Ya ce abin ya wuce gona da iri wanda ya ke bukatar daukar matakin gaggawa don dakile faruwar matsalar a nan gaba, cewar Vanguard.
Wane gargadi Aminu Bayero ya tura?
A cewarsa:
"Dole wannan mummunan dabi'a ta tsaya haka, ba za mu zuba ido ana sace yaranmu ana siyar da su ba sannan a sauya musu addini da kuma yare.
"Dole a tsaya tsayin daka don kawo karshen matsalar, abin ya wuce gona da iri, matsalar ba za ta dakilu ba sai mun tashi tsaye.
"Shekarun baya hakan ya faru, yanzu ma ya sake faruwa, ba mu san adadin yara nawa aka sace kuma aka siyar ba."
Idan ba manta ba, a ranar 27 ga watan Disamba ne rundunar 'yan sanda a jihar ta bankado gungun masu garkuwa da kuma siyar da yaran.
'Yan sanda sun gana da 'yan daba 52 a Kano
A wani labarin, rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta gayyaci wasu kasurguman 'yan daba 52 don tattaunawa da su.
'Yan dabar da aka gayyata sun fito ne daga yankin Kwanar Dangora da ke karamar hukumar Kiru a jihar.
Asali: Legit.ng