Jerin Mutum 10 da Suka Fi Kowa Arziki da Adadin Dukiyarsu a Watan Junairun 2024
- Arzikin kasurguman masu kudi 10 da ake ji da su a duniya ya karu da $30 a farkon shekarar nan
- Elon Musk yana da sama da $250b a lissafin Forbes, mai bi masa shi ne Bernard Arnault da danginsa
- Bill Gates ya sauko a farkon 2024, Mark Zuckerberg mai kamfanin Facebook ya zarce shi da $3m
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.
Su wanene su ka fi kowa kudi a 2024?
1. Elon Musk
Elon Musk bai da sa’a a duniya a yau, mujallar Forbes ta ce shugaban kamfanin na Tesla da kuma dandalin X ya mallaki fam $251bn.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2. Bernard Arnault
Bernard Arnault shi ne na biyu, ya yi arziki da harkar kwalliya. Shugaban na Louis Vuitton, Christian Dior da sauransu ya mallaki $197bn.
3. Jeff Bezos
Jeff Bezos wanda ya kafa Amazon tun 1994 yana cikin wadanda ake damawa da su har yau. Rahotanni sun ce yana da fiye da $172bn.
4. Larry Ellison
Dukiyar Larry Ellison ta ragu a sakamakon karyewar hannun jarin Oracle. Shi ne na hudu a duniya da $135.3bn, dukiyarsa ta ragu da $11bn.
5. Mark Zuckerberg
Mark Zuckerberg ya samu karin arziki sosai a halin yanzu, ya zama na biyar da bayan a watan Disamba shi ne na bakwai a duniya da $122m.
6. Bill Gates
A 1987 aka fara kawo Bill Gates a biliniyoyin da ake ji da su, daga 1995 zuwa 2017 ya sha gaban kowa, a Junairun nan ana lissafin yana da $119m.
7. Warren Buffett
Tun yana yaro Warren Buffett ya san harkar kudi. Techeconomy ta ce tsohon mai shekara 93 ne na bakwai a duniya da sama da $120m.
8. Larry Page
Larry Page da Sergey Brin suka kafa Google a 1998 har yanzu yana cikin manyan kamfanin. Dukiyar Page ta zarce $116m a shekarar nan.
9. Sergey Brin
Kamar Larry Page, tsohon abokin aikinsa, Sergey Brin mai shekara 50 ya tara $111bn. yana cikin masu juya kamfanin Alphabet masu google.
10. Steve Ballmer
Steve Ballmer abokin karatun Bill Gates ne a jami’ar Harvard University kuma ya yi aiki a Microsoft. Attajirin da ya shiga NBA yana da $110m.
Attajiran duniya a 2023
A bara ana da labarin yadda Elon Musk ya sullobo ya ba Bernard Arnault wuri a jeringiyar mutanen da suka fi kudi na wani gajeren lokaci.
A lokacin ne aka ji cewa dukiyar Bernard Arnault nunka ta Bill Gates sau biyu har da doriya a sakamakon rabuwa da ya yi da mai dakinsa.
Asali: Legit.ng