Faransa Ta Kakaka Doka Marar Dadi Kan Daliban Najeriya Masu Zuwa da Iyalansu, Ta Fadi Dalili

Faransa Ta Kakaka Doka Marar Dadi Kan Daliban Najeriya Masu Zuwa da Iyalansu, Ta Fadi Dalili

  • Kasar Faransa ta kafa wata sabuwar doka da zata dakile daliban Najeriya da sauran kasashe zuwa da iyalansu kasar
  • Shugaba Emmanuel Macron na Faransa da mataimakiyar Majalisar Dokoki, Marine Le Pens duk sun goyi bayan dokar
  • Hakan na zuwa ne kwanaki bakwai kacal bayan wasu sun yi zanga-zangar kin amincewa da dokar hana daliban zuwa da iyalansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Paris, Faransa – Majalisar kasar Faransa ta kafa sabuwar doka kan daliban Najeriya da sauran kasashen duniya.

Majalisar ta amince da dokar hana daliban Najeriya da sauran kasashe zuwa da iyalansu kasar, Legit ta tattaro.

Faransa ta kakaba doka kan daliban Najeriya
Faransa ta saka dokar hana daliban Najeriya zuwa da iyalansu. Hoto: David Butow/Corbis: An yi amfani da hoton don misali ne kawai. Wadanda ke hoton ba su da alaka da batun da ake magana.
Asali: Getty Images

Wane mataki Faransa ta dauka kan daliban Najeriya?

Kara karanta wannan

Nazarin shekara: Shugaba Tinubu da wasu manya jigan-jigan siyasa da suka samu gagarumar nasara a 2023

Shugaba Emmanuel Macron da mataimakiyar Majalisar Dokoki, Marine Le Pens duk sun goyi bayan dokar cikin aminci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na zuwa ne kwanaki bakwai kacal bayan wasu sun yi zanga-zangar kin amincewa da dokar hana daliban zuwa da iyalansu.

Gwamnatin Faransa ta yi wannan doka ce mai tsanani saboda dakile iyalan daliban ci gaba da cin gajiyar wasu abubuwa a kasar, cewar Daily Trust.

Wasu ka'idoji kuma dokar ke dauke da su a Faransa?

Har ila yau, a cikin dokar ta hana kulle kananan yara a gidajen gyaran hali ko kuma wurin hukunta kananan yara, kamar yadda Punch ta tattaro.

Dokar ta kuma bambance tsakanin ‘yan kasa da kuma baki har ma da wadanda ke zaune a kasar ba tare da ka’ida ba.

Marine Le Pens ta goyi bayan dokar ce a ranar Litinin 18 ga watan Disamba inda ta ce wannan gagarumar nasara ce a kasar.

Kara karanta wannan

Rusa zaben Abba Kabir: Jerin hukunce-hukuncen kotu 4 da suka bai wa kowa mutane a 2023

Yadda ‘yan Najeriya zasu yi karatu kyauta a Faransa

A wani labarin, Ofishin Jakadancin Faransa ya sanar da karbar takardun karatun dalibai a bangarori da dama don karatun digiri na biyu.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin 6 ga wata Disamba inda aka rufe ranar 15 ga watan Disamba.

Tallafin karatun kamar yadda sanarwar ta fitar zai ba da kudaden sufuri da alawus don samar da sauki ga daliban a kasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.