Fafaroma Francis Ya Fadi Wurin da Ya Ke Son a Birne Shi Bayan Ya Mutu

Fafaroma Francis Ya Fadi Wurin da Ya Ke Son a Birne Shi Bayan Ya Mutu

  • Fafaroma Francis ya bar wasiyya cewa a birne shi a makabartar Basilica da ke birnin Rome, maimakon St. Peter's da aka saba binne masu mukamin
  • A wannan makon ne Francis ke cika shekaru 87 da haihuwa, wanda kuma ke fama da matsananciyar rashin lafiya a 'yan shekarun nan
  • Sai dai babban malamin addinin ya ce zai iya yin murabus idan har jikin nashi ya tsananta, kamar yadda Benedict ya yi a zamanin sa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Rome, kasar Italiya - Shugaban darikar Katolika na duniya, Fafaroma Francis ya zabi a birne shi a cikin makabartar Basilica da ke birnin Rome, kasar Italiya maimakon makabartar St Peter's da ke birnin Vatican.

Kara karanta wannan

Kwallaye 50 a cikin shekarar 2023: Har yanzu da sauran Cristiano Ronaldo

"Tuni aka gyara wajen, a Santa Maria Maggiore na ke so a binne ni," cewar Fafaroma, wanda ke cika shekaru 87 a wannan makon.

Fafaroma Francis ya bar wasiyyar inda ya ke so a birne shi idan ya mutu
Fafaroma Francis ya zabi a birne shi a cikin makabartar Basilica da ke birnin Rome, kasar Italiya. Hoto: @Pontifex
Asali: Twitter

Bayan shekaru 100 za a binne Fafaroma a Vatican

A hirarsa da gidan talabijin na N+ da ke garin Mexico, Fafaroma ya bayyana shirinsa na ziyartar Belgium a shekarar 2024 da kuma ziyartar Argentina da Polynesia.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan mataki da Francis ya dauka na nuni da cewa shi ne zai zama Fafaroma na farko da za a binne a wajen garin Vatican, bayan shafe sama da shekaru 100.

Leo XIII shi ne na karshe da aka binne a St Peter's a shekarar 1903, kabarinsa na nan a makabartar ginin St. John a Rome, The Punch ta ruwaito.

Alakar Fafaroma Francis da Santa Maria Maggiore

Santa Maria Maggiore na daga cikin manyan gine-ginen da ake binne Fafaroma idan ya mutu a Rome, kuma a cikinsu ne Francis ya ce ya ke so a binne shi a ciki.

Kara karanta wannan

Kano: EFCC ta gurfanar da ma'aurata kan handame miliyan 410, ta bayyana yadda abin ya faru

Ya kan ziyarci gini a wasu ranakun Lahadi idan har ya ziyarci Rome kafin ya zama Fafaroma, tun bayan zafensa a shekarar 2013 ya ke addu'a a wajen.

A halin yanzu dai Fafaroma Francis na fama da rashin lafiya da ta karuwa a shekarun nan, lamarin da ya tilasta shi soke zuwa taron COP28 da aka yi a Dubai.

A wata tattaunawa, Francis ya ce zai iya daukar matakin da magabancinsa Benedict ya dauka na yin murabus idan har jikin nasa ya tsananta.

Luwadi ba laifi ba ne, cewar Fafaroma Francis

A watan Janairun 2023 ne Legit Hausa ta ruwaito maku rahoton wani jawabi na Fafaroma Francis wanda ya ke cewa luwadi ba laifi ba ne, abin da ya jawo kumfar baki a duniya.

Shugaban cocin Katolika na duniya ya soke dokokin da suke hukunta masu luwadi, inda ya ce ubangijinsu bai nuna wariya kan wasu jinsin mutane ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.