Kotu Ta Yi Hukunci Kan Karar da Sojin Nijar Su Ka Shigar da Tinubu, ECOWAS, Ta Ba da Dalilai
- Yayin da sojin Nijar su ka shigar da kara kan Tinubu da ECOWAS, kotun ta raba gardama kan takunkumi a kasar
- Kotun ta yi watsi da korafin kasar Nijar inda ta ce ba ta da hurumin neman wani hakki a kungiyar da ba ta ciki
- Tinubu da ECOWAS a ranar 8 ga watan Agusta sun kakaba wa sojin Nijar takunkumi bayan sun kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja – Kotun Kungiyar ECOWAS ta yi hukunci kan karar da sojojin Nijar su ka shigar da Shugaba Tinubu da ECOWAS.
Kotun wacce ke zamanta a Abuja a jiya Alhamis 7 ga watan Disamba ta kori karar da sojin Nijar din su ka shigar saboda rashin hujjoji, cewar VOA.
Wane hukunci kotun ta yi kan Tinubu, ECOWAS?
Tinubu da ECOWAS a ranar 8 ga watan Agusta sun saka wa sojin Nijar takunkumi bayan sun kifar da gwamnatin Mohamed Bazoum.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sojin sun shigar da kara kotu inda su ke kalubalantar takunkumin tare da nuna cewa hakan ya jawo matsala ga kasar da kuma mutanenta.
Daga cikin takunkumin akwai yanke wutar lantarki zuwa kasar wanda hakan ya jawo karancin abinci da magani a Nijar.
Sojin sun bukaci kotun ta tilasta Tinubu da ECOWAS su yi gaggawar janye wannan takunkumi da su ka saka.
Mene alkalin kotun ke cewa kan Tinubu, ECOWAS?
Yayin hukuncin, Mai Shari’a, Edward Asante ya ce kasar da ba ta cikin kungiyar ba ta da hurumin neman kotun kungiyar wani hakki.
Ya ce:
“Kasar da ta kasance bayan juyin mulki ba ta da hurumin shigar da kungiyar ECOWAS kara don neman wani hakki.”
Kotun ta kara da cewa Nijar ta gaza kawo hujjoji kan irin matsalar da takunkumin ya jawo a kasarta, cewar Premium Times.
Bazoum ya koka kan abinci
A wani labarin, hambararren shugaban kasar Nijar, Mohamed Bazoum ya koka kan irin gabzar da ake ba shi yayin da ya ke hannun sojoji.
Bazoum ya ce babu abin da su ke ba shi illa busasshiyar shinkafa inda ya ce babu ruwa mai tsafta da kuma magani.
Asali: Legit.ng