Uganda: Tsohuwa ’Yar Shekaru 70 da Ta Haifi Tagwaye Ta Hanyar IVF Ta Kafa Tarihi a Afrika

Uganda: Tsohuwa ’Yar Shekaru 70 da Ta Haifi Tagwaye Ta Hanyar IVF Ta Kafa Tarihi a Afrika

  • Asibitin karbar haihuwa da kula da mata na kasa-da-kasa da ke Uganda ya sanar da cewa dattijuwa 'yar shekaru 70 ta haihu a asibitin
  • A cewar asibitin a shafinsa na Facebook sun yi amfani da fasahar IVF akan dattijuwar, kuma tana cikin koshin lafiya bayan haihuwar
  • Da wannan ne matar ta shiga cikin tarihi na zama mace dattijuwa da ta haihu a Afrika, bayan shafe shekaru 70

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kampala, kasar Uganda - Wata jarumar dattijuwa 'yar shekaru 70 ta jefa mutane da dama cikin mamaki bayan da ta haifi tagwaye a wani asibiti da ke Uganda.

A wata sanarwa a shafin Facebook, asibitin haihuwa da kula da mata na kasa-da-kasa da ke Uganda ya ce Safina Namukwaya ta haifi tagwayen a ranar 25 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Kotu ta dauki mataki kan matar da ta lakadawa mijinta duka saboda yana hira da yan mata

Asibiti/Uganda/Haihuwa/Dattijuwa/Tagwaye
Asibitin ya yi amfani da fasahar IVF har dattijuwar ta haihu, kuma matar da jariran na cikin koshin lafiya. Hoto: Women's Hospital International and Fertility Centre
Asali: Facebook

Safina Namukwaya ta kafa tarihi na tsohuwar mata da ta haihu a Afrika, bayan haihuwar tagwaye namiji da mace, asibitin ya ce matar da yaran na cikin koshin lafiya, rahoton jaridar Tuko.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da asibitin Uganda ya ce kan wannan nasara

Matar ta samu ciki ne bayan da asibitin ya yi amfani da fasahar IVF na sanya kwayar halitta a mahaifarta, abin da ya shiga kundin tarihin asibitin.

"Mun kafa tarihi a Afrika. Muna bikin cika shekaru 20 da kafuwa, mun yi nasarar kula da dattijuwa 'yar shekaru 70 har ta haifi tagwaye, ta shiga tarihi ita ma.
"Jariran mace da namiji, ba iya nasarar fasahar IVF suka nuna ba, sun kuma tabbatar da cewa za a iya rainon kwayar halitta cikin mahaifa komai tsufanta a Afrika."

A cewar sanarwar da asibitin ya yi a shafinsa na facebook.

Kara karanta wannan

Ministoci 9 sun tashi da kaso mafi tsoka a kasafin kudin naira tiriliyan 27 da Tinubu ya gabatar

Menene IVF?

A wani bayani daga asibitin Mayo Clinic, ya yi nuni da cewar akwai rikitarwa a fasahar IVF wacce ke kai ga samar da ciki a mahaifar mace ke bukatar taka tsan-tsan.

Asibitin ya ce ana kuma amfani da fasahar wajen dakile jarirai daga daukar wata cuta daga mahaifiyarsu.

Jarumi Abale ya samu karuwar diya mace

A wani labarin, shahararren jarumi a masana'antar shirya fina-finan Hausa, Daddy Hikima, ya samu karuwar diya mace, ya wallafa hotunanta a shafin sa na Instagram, Legit Hausa ta ruwaito.

A ranar 27 ga watan Janairun wannan shekarar ne aka dauka auren jarumin da masoyiyarsa Maryam, auren da ya samu halartar manyan jarumai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.