Juyin Mulki a Kasar Saliyo? Abinda Muka Sani Yayin da Gwamnati Ta Sanya Dokar Hana Fita

Juyin Mulki a Kasar Saliyo? Abinda Muka Sani Yayin da Gwamnati Ta Sanya Dokar Hana Fita

  • Ana fargabar juyin mulki a Saliyo, yayin da wasu ƴan bindiga da ba a san ko su waye ba suka kai hari a barikin soji da ke Freetown
  • Daga baya gwamnatin Saliyo ta kafa dokar hana fita a faɗin ƙasar, inda ta bukaci ƴan ƙasar da su kasance a gida
  • Shugaba Julius Maada Bio, ya tabbatar wa jama'a cewa jami’an tsaro sun fatattaki maharan, tare da dawo da kwanciyar hankali, ya kuma jaddada aniyarsa ta kare dimokuraɗiyya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Freetown, Saliyo - Ana fargabar juyin mulki a ƙasar Saliyo, bayan wani harin da aka kai barikin sojoji.

Rahotanni da dama sun nuna cewa wasu ƴan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari a barikin sojoji tare da yunkurin kutsawa cikin rumbun ajiye makamai a babban birnin ƙasar, Freetown, a ranar Lahadi, 26 ga watan Nuwamba.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: Gwamna Fubara ya sake kalubalantar Nyesom Wike

Fargabar juyin mulki a Saliyo
Gwamnatin Saliyo ta sanya dokar hana fita Hoto: ISSOUF SANOGO/AFP, Mychal Watts
Asali: Getty Images

Gwamnatin Saliyo ta kafa dokar hana fita a faɗin kasar domin daƙile wannan harin da aka kai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Harin Saliyo: An sanya dokar hana fita

A cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, ministan yaɗa labarai na Saliyo, Chernor Bah, ya buƙaci dukkanin ƴan ƙasar da su kasance a gida.

A cewar rahoton Reuters, Bah a cikin sanarwa ya bayyana cewa:

"Da sanyin safiyar Lahadi wasu mutane da ba a san ko su wanene ba sun yi yunƙurin kutsawa cikin ma'ajiyar kayan yaki na sojoji a barikin Wilberforce, an kuma hana su."
"An ayyana dokar hana fita a faɗin ƙasa nan take...Muna shawartar jama'a da du kasance a cikin gida."

Shugaban ƙasar Saliyo Julius Maada Bio ya yi jawabi ga ƴan ƙasar

A halin yanzu, Shugaba Julius Maada Bio na Saliyo ya yi wa ƴan ƙasar jawabi game da halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Jiragen yakin rundunar sojojin sama sun halaka kasurgumin shugaban yan ta'addan Boko Haram

A cikin wata sanarwa da ya sanya a shafinsa na X, shugaban ya ce an kai hari a barikin sojoji da ke Wilberforce a birnin Freetown.

Sai dai ya ce jami’an tsaro sun fatattaki ƴan bindigan, inda ya ce an samu kwanciyar hankali.

Shugaban na Saliyo ya ƙara da cewa haɗaɗɗiyar tawagar jami'an tsaro za ta kori ragowar ƴan tawaye da suka tsere.

Shugaba Maada Bio ya ce ya kuɗuri aniyar kare dimokuradiyya a Saliyo, ya kuma buƙaci ɗaukacin ƴan ƙasar da su haɗa kai domin cimma ƙudurin.

Yadda aka sake zaɓen Maada Bio a zaɓen Saliyo da ake taƙaddama a kai

An sake zaɓen Shugaba Bio a watan Yunin 2023 a zaɓe mai cike da taƙaddama, wanda babban ɗan takarar adawa ya ƙi amincewa da sakamakonsa.

Al Jazeera ta ruwaito cewa masu sa ido na ƙasa da ƙasa sun yi tir da "rashin gaskiya" a zaɓen. Tuni dai al'amuran siyasa a ƙasar ta yammacin Afirka ke ci gaba da taɓarɓarewa.

Kara karanta wannan

Babbar magana: Yan bindiga sun buɗe wuta, sun yi garkuwa da shugaban APC a jihar arewa

Zanga-zangar adawa da gwamnati a watan Agusta ta yi sanadiyyar mutuwar jami'an ƴan sanda shida da kuma fararen hula aƙalla 21.

Shugaba Maada Bio ya bayyana zanga-zangar a matsayin yunkurin juyin mulki.

Sojoji Sun Yi Yunkurin Juyin Mulki a Burkina Faso

A wani labarin kuma, wasu sojoji a ƙasar Burkina Faso sun yi yunƙurin kifar da gwamnatin sojojin ƙasar.

Gwamnatin sojojin ƙasar ce dai ta bayyana hakan inda ta tabbatar da cewa sojoji sun daƙile yunƙurin da aka yi na yin juyin mulki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng