Kasashe 10 da suka fi talauci a nahiyar Afirka

Kasashe 10 da suka fi talauci a nahiyar Afirka

Nahiyar Afirka tana da yanayi mai kyau. Akwai kasar noma mai kyau tare da ma'adinai na karkashin kasa amma duk da hakan akwai kasashe da dama dake fama da talauci.

Ko kan san wacce kasa ce tafi talauci a Afirka a shekarar 2018? Cigaba da karatu don samun amsar tambayar.

Ana auna arzikin kasashe ne (wato GDP) ta hanyar yin raskanawar abinda kowanne mutum ya kashe a kasar da abinda kudin shigar gwamnati da cinkin da 'yan kasuwa da masana'antu su kayi da kuma kudaden da aka samu ta hanyar fitar da kayayaki kasashen waje.

A takaice ana sanin GDP ne idan an harhada kudaden da kasar ke samu a jumlace.

DUBA WANNAN: An yiwa manya-manyan sojojin Najeriya canjin ayyuka

Ga jerin kasashen ta suka fi talauci a Afirka kamar yadda kididigar bankin duniya tayi a shekarar 2018.

Kasashe 10 da suka fi Talauci a nahiyar Afirka
Kasashe 10 da suka fi Talauci a nahiyar Afirka

10. Gambia (GDP - $473)

Gambia kasa ce data dogara da kiwo da kuma ma'adanan kasa wajen gina tattalin arzikinta, duk da cewa Gambia tafi sauran kasashe 9 da ke biye mata a jerin wajen GDP, kasar har yanzu tana dogara ne ga taimakon da kasashen ketare ke bata.

09. Liberia (GDP - $455)

Kamar sauran kasashen Afirka, Liberia ta dogara ne da noma da albarkatun kasa. Sai dai bayan yakin basasar kasar abubuwa sun tabarbare a kasar hakan ya kara ruruta talauci a kasar.

08. Jamhuriyar Demokradiyar Congo/DRC (GDP - $444)

Al'ummar kasar na wahalar samun aiki duk da cewa akwai kasar noma da gandun daji da sauran hanyoyin samar da arziki. An kiyasta GDP din Congo misalin dalan Amurka 444 a shekarar 2018.

07. Somalia (GDP - $434)

Ba za ayi mamakin ganin Somalia cikin kasahe mafi talauci ba saboda kasancewar kasar ta kwashe shekaru 30 tana gwabza yakin basasa kuma a sojoji ke mulkin kasar. Tattalin arzkin kasar ya ki habaka saboda sun dogara ne da kasashen waje, kiwo da sadarwa.

06. Madagascar (GDP - $401)

Duk da cewa kasar na cigaba da habaka fanin mona da ma'adinanta, har yanzu ta gaza samun masu saka hannun jari saboda rikice-rikicen siyasa. GDP din kasar bai wuce dallan Amurka 401 ba.

05. Central African Republic/CAR (GDP - $382)

Al'ummar kasar sun kasa cin moriyar albarkatun kasa da suke dashi kamar zinari da katako saboda shekarun da aka kwashe ana yaki ya haifar da matsananciyar rashawa a kasar kuma hakan ke kara musu koma baya.

4. Mozambique (GDP - $382)

An kawo karshen yakin basasar kasar da aka kwashe shekaru 15 anayi a 1992, sai dai tun daga wannan lokacin babu wata cigaba sosai da aka samu. Mafi yawancin al'ummar kasar manoma ne sai dai 7% filin kasar ne ake iya nomawa, hakan yasa ba'a samun wasu kudaden shiga da zai iya habaka tattalin arzikin kasar.

3. Nijar (GDP - $364)

Nijar kasa ce dake yammacin Afirka kuma itace kasa ta 3 mafi talauci a Afirka. Kasar ta dogara da noma ne sai dai mafi yawancin amfanin gonar akan sayar dasu ne ga sauran kasashen Afirka masu tasowa hakan yasa tattalin arzikin kasar baya cigaba sosai.

2. Malawi (GDP - $300)

Malawi itace kasa ta biyu mafi talauci a Afirka saboda matsalolin da kasar ke fama dashi cikin shekarun da suka gabata. Al'umma kasar na fama da karancin asibitoci da makarantu. Yawancinsu manoma ne sai dai suna fama da rashin lafiya daban-daban.

1). Burundi (GDP - $285)

Burundi itace kasar da tafi talauci a Afirka a wannan jerin namu. An kiyasta GDP din kasar a matsayin dallan Amurka 285. Galibin mazauna kasar manoma ne sai dai basu da kayayakin noma na zamani kuma har yanzu kasar na farfadowa daga yakin basasa da ya afku a baya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel