An Fara Ganin Fa’idar Ziyarar Tinubu, Najeriya da Saudi Arabiya Sun Sa Hannu a Yarjejeniya
- Ministan Najeriya da takwaransa na Saudi Arabiya sun rattaba hannu a wata yarjejeniya da kasashen biyu su ka shiga
- Sanata Heineken Lokpobiri ya yi bayanin yadda yarjejeniyar za ta taimakawa tattalin arzikin kasa da al’ummar Najeriya
- Hadimin Ministan ya nuna a dalilin haka, za a samu cigaba a harkar mai da gas, kuma mutane za su samu ayyukan yi a kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Saudi - Najeriya da gwamnatin Saudi Arabiya sun shiga wata yarjejeniyar harkar mai da gas da ake sa ran zai taimakawa kasashen biyu.
A yammacin Alhamis, The Nation ta fitar da rahoto cewa gwamnatocin Najeriya da na Saudiyya sun rattaba hannu a wata takardar MoU.
Wannan yarjejeniya za ta bunkasa bincike da nazari, kawo cigaba, yada ilmi da fito da tsare-tsaren da za su horar da mutane a Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Heineken Lokpobiri v Abdulaziz bin Salman a Saudi
Karamin Ministan harkar mai, Sanata Heineken Lokpobiri ya sa hannu a madadin Najeriya, sai Abdulaziz bin Salman a madadin kasar Saudi.
Yarima da Heineken Lokpobiri sun sa hannu ne a birnin Riyadh kamar yadda wani hadimin Ministan man, Nneamaka Okafor ya shaida a jiya.
Ta ya Najeriya za ta amfana da MOU da kasar Saudi?
Vanguard ta ce Mista Nneamaka Okafor ya fitar da jawabi ya na mai bayanin amfanin da yarjejeniyar za ta yi wa Najeriya da mutanenta.
"Daya daga cikin muhimman amfanin fitacciyar yarjejeniyar nan ita ce za ta taimaka wajen yada fasaha tsakanin juna.
Yayin da Saudiyya ta cigaba ta fuskar fasaha a bangaren hako mai da gas, Najeriya za ta amfana sosai da wannan ilmi.
Cakuduwar sanin aiki zai taimaka wajen kara kyawun aikin Najeriya wanda zai jawo karuwar mai da ciniki.
Ana sa ran wannan MOU za ta yi sanadiyyar jawo masu hannun jari zuwa Najeriya su shiga cikin harkar mai da gas."
- Nneamaka Okafor
Lokpobiri ya ce yarjejeniyar za ta taimaka wajen tsaida farashin mai da samar da ayyuka. Bola Tinubu ne yake rike da kujerar babban Minista.
Tinubu ya nada mukami
A jiya aka samu labari cewa Rinsola Abiola ta samu aikin babban mai bada shawara a harkar shugabanci da 'yan kasaa gwamnatin Bola Tinubu.
Shugaban karamar hukumar Abeokuta ta Arewa, Prince Adebayo Abdussalam Ayorinde ya tabbatar da haka a wani jawabi da ya fitar a X.
Asali: Legit.ng