Isra'ila/Hamas: A Karshe, Isra'ila Ta Ji Korafe-korafe, Ta Fitar da Sanarwa Kan Tsagaita Wuta
- A karshe, Isra'ila ta yanke hukuncin tsagaita wuta na wasu awanni a Arewacin Gaza yayin da ake ci gaba da rikici
- Isra'ila za ta tsagaita wuta na awanni hudu a ko wace rana don ba da damar ficewa na fararen hula daga Gaza
- Wannan na zuwa ne yayin da ake ci gaba da gwabza yaki tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas
Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Tel Aviv, Israila - Yayin da ake ci gaba da rikici tsakanin isra'ila da kungiyar Hamas, kasar Isra'ila ta dauki matakin tsagaita wuta.
Isra'ila ta dauki matakin tsagaita wuta na awanni hudu ko wace rana don bai wa fararen hula damar ficewa daga Arewacin Gaza.
Waye ya bayyana sanarwar tsagaita wuta?
Fadar Gwamnatin Amurka ce ta bayyana haka a yau Alhamis 9 ga watan Nuwamba, cewar NBC News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sai dai Joe Biden na Amurka ya bayyana cewa ba zai yi yu a tsagaita wutar gaba daya ba.
Biden ya sha matsawa Fira Ministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu kan tsagaita wutar na wani lokaci, Daily Trust ta tattaro.
Meye sanarwar ke cewa kan matakin tsagaita wutar?
Kakakin kwamitin tsaron kasar John Kirby ya ce:
"Isra'ila za ta fara aiwatar da dakatar da bude wuta ta tsawon awanni hudu a yankunan arewacin Gaza a kowace rana, tare da bayar da sanarwar awanni uku kafin hakan,"
"Mun yi amannar cewa wannan dakatarwar wani mataki ne na hawa madaidaiciyar hanya.
"Wannan zai kawo sauki musamman don tabbatar da cewa fararen hula za su samu damar tserewa zuwa yankuna masu aminci da ke nesa daga inda ake yakin."
Wannan na zuwa ne bayan shafe fiye da wata guda ana gwabza yaki tun bayan harin bazata da kungiyar Hamas ta kai kan Isra'ila.
Gumi ya bude asusun tallafawa Falasdinawa
Kun ji cewa, Sheikh Ahmed Gumi ya bude asusun da za a taimakawa Falasdinawa a Gabas ta Tsakiya.
Gumi ya yi wannan kudiri ne yayin da ake ci gaba da rikici tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas a yankin Falasdinu.
Asali: Legit.ng