Duniya Ta Yi Allah Wadai da Israila a Kan Kashe Fiye da Bayin Allah 500 a Asibiti

Duniya Ta Yi Allah Wadai da Israila a Kan Kashe Fiye da Bayin Allah 500 a Asibiti

  • An kai hari a wani tsohon asibiti da ake kula da marasa lafiya a zirin Gaza, hakan ya yi sanadiyyar mutane fiye da 500
  • Ana zargin sojojin Israila ne su ka yi wannan danyen aiki da nufin hallaka dakarun Hamas da su ka labe a asibitin
  • Daga baya Gwamnatin Israilar ta nuna babu ruwanta, ta zargi kungiyar Hamas wanda ta fara kai mata munanan hari

Gaza - A halin yanzu, suka kurum sojojin kasar Israila su ke sha a sakamakon wani mummunan hari da aka kai a asibitin Al-Ahli a Gaza.

Wannan asibiti ya na cikin tsofaffin asibitocin da kiristoci su ka kafa a yankin, Al Jazeera ta ce mutane sama da 500 bam ya hallaka a jiya.

Wani mutumi da aka yi hira da shi, ya shaidawa duniya yadda ake yi masu ruwan bama-bamai, ana kashe mutane a sakamakon harin Hamas.

Kara karanta wannan

“Na Tsorata”: Wani Dan Najeriya Ya Koka Yayin da Ya Ci Karo Da Wata Halitta a Janaretonsa, Ya Saki Bidiyo

Gaza.
Israila ta 'kashe' mutane a asibiti a Gaza Hoto: www.globalministries.org
Asali: UGC

Israila ta na kisa a zirin Gaza

A cewarsa, kowa ya na cikin dar-dar a zirin Gaza, ya kara da cewa ya na jin karan tashin bam a wajen gidansa, kullum abin ya na kara muni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Khamis Elessi wanda fitaccen Likita ne a kasar Falasdin, ya tabbatar da wannan hari a yammacin Talata, ya ce roka ta hallaka mutane barkatai.

Ana zargin dakarun Israila ba su kyale har wuraren da fararen hula da masu jinya su ke ba, abin da musulmai da sauran al'umma su ke tir da shi.

Majalisar dinkin duniya ta soki Israila

Hakan ta so zo dole aka ji shugaban majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres a kasar Sin ya na sukar hare-haren da ake kai wa mutanen Gaza.

Guterres ya ce ta’adin Hamas bai ba Israila lasisin kashe wadanda babu ruwansu ba.

Kara karanta wannan

Gwamnati Ta Tsaida Lokacin da Za a Fara Biyan Ma’aikatan N-Power Albashin Wata 9

Gaza: Netanyahu ya ce aikin Hamas ne

CNN ta ce Firayim Ministan Israila Benjamin Netanyahu ya fito ya na zargin ‘yan kungiyar Hamas da daukar nauyin ta’adin da aka yi a asibitin.

Amma kafin mutane su soki harin, kasar Israila ta nuna sojojinta ne su ka harbawa asibitin bama-bamai saboda ya zama mafakar dakarun Hamas.

Sarkin Musulmi ya yi tir da Israila

Kamar yadda rahoto ya zo,Shugabannin majalisar musulman Najeriya sun zargi dakarun Israila da kisan kare dangi a kan mutanen Falasdina.

Mai alfarma Sultan Abubakar Sa’ad III ya caccaki bayan ganin Falasdinawan da ake kashewa musamman a zirin gaza a 'yan kwanakin bayan nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

Online view pixel