Gaza: Fafaroma Ya Tsawata, Saudi Ta Kira Taro a Kan Yakin Israila da Falasdinu

Gaza: Fafaroma Ya Tsawata, Saudi Ta Kira Taro a Kan Yakin Israila da Falasdinu

  • Jorge Mario Bergoglio ya na ganin babu dalilin a kashe wadanda ba su yi laifin komai ba a rikicin da ake yi a yankin Gaza
  • Fafaroma Francis ya yi kira ga sojojin Israila da su guji hallaka mata, tsofaffin, yara da marasa lafiya babu gaira babu dalili
  • A makon nan kasashen Musulmai da ke karkashin kungiyar OIC za su yi zama a kan hare-haren da ake kai wa ‘yan Falasdinu

Gaza - A jiya ne Fafaroma Francis ya tsoma bakinsa, ya yi magana a game da ta’adin da kasar Israila ta ke yi wa mutanen yankin Gaza.

Gidan jaridar Reuters ta rahoto shugaban mabiya darikar Katolikan Kiristoci ya na sukar zubar da jinin kananan yara da mata da ake yi.

Fafaroma Francis ya yi kira da a bada dama domin masu bada agaji su iya kai a zirin Gaza, inda Israila ta ke ikirarin ganin bayan Hamas.

Kara karanta wannan

Sarkin Musulmi Ya Soki Amurka a Kan Goyon Bayan Israila Wajen Hallaka ‘Yan Gaza

Gaza.
Yakin da ake yi a Gaza Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

An rasa rayuka a Israila da Falasdin

Shugaban kiristocin ya ce wajibi ne a kula da dokokin kare ‘dan adam yayin da ake yakin, tuni Iran ta gargadi kasar Yahudawan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cikin sama da mako guda da ake zargin ‘yan Hamas sun hallaka Israiliyawa fiye da 1, 300, an kuma rasa Falasdinawa akalla 2, 300.

A yayin da ya ke magana a wajen taron addu’o’i da aka gudanar a filin Waliyyi Peter a birnin Rome, Fafaroma ya bukaci a kai taimako.

"Ina matukar kira da cewa bai kamata rikicin ya aukawa kananan yara, marasa lafiya, tsofaffin, mata da duk masu fararen kaya ba.
"An samu mace-mace sosai, ka da a cigaba da zubar da jinin wadanda ba su yi laifi ba, a kasa mai tsarki, ko Ukraine ko wani wuri ba.
"Abin ya isa haka nan. Har kullum yaki ba nasara ba ce."

Kara karanta wannan

Isra'ila/Falasdinu: Iran Ta Tura Gargadi Ga Isra'ila Kan Gaza, Ta Bayyana Matsayarta

- Fafaroma Francis

OIC ta kira kasashen Musulmai

A jawabin da aka samu a shafinta, kungiyar OIC ta musulman Duniya ta kira taron gaggawa da za ayi a game da mummunan yakin da ake yi.

Saudi Arabiya ta nemi ayi wannan zama a ranar Laraba, 18 ga watan Oktoba 2023 a hedikwatar OIC da ke Jeddah domin a tattauna kan batun.

Hamas za ta ceto Musulmai a Israila

Kwanakin baya an samu labari cewa Abdel-Latif al-Qanoua ya yi alkawari kungiyar Hamas za ta kubutar da Musulmai daga hannun Israilawa.

Hamas sun kai wa kasar Israila mamaya bayan shekara da shekaru ana kashe Falasdinawa, an rasa rayuka sosai a hare-haren da aka kai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng