Yakin Isra'ila-Falasdinu: Sojojin Isra'ila Sun Kutsa Cikin Zirin Gaza
- Dubban mutane fara rige-rige domin tsira da rayukansu bayan sanarwar da sojojin Isra'ila suka yi na ƙaddamar da farmaki a cikin Gaza cikin sa'o'i 24
- Sai dai rahotanni sun tabbatar da cewa tuni sojojin Isra'ila na ƙasa suka kutsa kai cikin zirin Gaza a wani yunkuri na kakkabe ƙungiyar Hamas mai kishin Islama
- An tattaro cewa dubunnan Falasdinawa, sun tsere daga arewacin Gaza zuwa yankin Kudancin domin tsira
Gaza, Falasdinu - Rahotanni da ke fitowa sun tabbatar da cewa rundunar sojin Isra'ila ta sanar da cewa dakarunta na ƙasa sun fara aiki a cikin zirin Gaza.
A cewar Aljazeera, sojojin Isra'ila sun yi gargadi a ranar Juma'a 13 ga watan Oktoba, inda suka baiwa mazauna yankin sa'o'i 24 su fice daga Arewacin zirin Gaza.

Asali: Getty Images
An yi amanna cewa dubban Falasdinawa ne suka tsere zuwa Kudancin zirin Gaza domin neman mafaka a daidai lokacin da sojojin Isra'ila ke da niyyar fara kai farmaki ta ƙasa kan kungiyar Hamas a matsayin ramuwar gayya kan harin da aka kai mafi muni a tarihin Isra'ila.

Kara karanta wannan
Bayan Ganin Kamun Ludayin Tinubu, Kiristocin Najeriya Sun Canza Tunani Kan Tikitim Musulmi da Musulmi
A halin da ake ciki dai ana ta mayar da martani a duk duniya dangane da yakin da ake yi tsakanin Isra'ila da Falasdinu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Zanga-zanga a birnin New York
A wani rahoto da tashar Aljazeera ta fitar a baya-bayan nan, daruruwan mutane ne suka yi dafifi da yawansu domin nuna goyon bayansu ga Falasdinawa a birnin New York na ƙasar Amurka.
An ga masu zanga-zangar a cikin adadinsu suna ɗaga tutocin Falasdinawa da alamun da ke cewa "Free Palastine".
An tattaro cewa wasu masu zanga-zangar sun riƙa rera waƙar cewa gwamnatin Amurka ta daina ba wa sojojin Isra'ila kuɗaɗe.
Saudiyya ta yi kira da a tsagaita wuta
Hakazalika, gwamnatin Saudiyya ta yi kira da a tsagaita buɗe wuta tare da nuna goyon baya ga Falasdinawa.
A babban masallacin Makkah, limamin masallacin Sheikh Osama bin Abdullah Khayyat ya zubar da hawaye yayin da yake jagorantar sallah yana mai cewa: Allah ya kare musulmin Palasɗinu.

Kara karanta wannan
Yakin Isra'ila/Falasdinu: Isra'ila Ta Yi Barazanar Datse Wuta, Ruwa da Fetur Kan Abu 1 Tak, Bayanai Sun Fito
Shehin Malamai Ya Yi Hasashen Rushewar Isra'ila
A wani labarin kuma, sanannen malamin addinin musulunci, Sheikh Mansur Isa Yelwa a wani karatu da ya gabatar ya hasko maganar da wani malamin Falasɗinawa ya taɓa yi a baya.
Marigayi Marigayi Sheikh Ahmad Yasseen ya taba yin hasashen cewa kasar Israila za ta ruguje nan da shekarar 2027 bayan ta balaga.
Asali: Legit.ng