Fasto Adeboye Ya Goyi Bayan Kasar Isra'ila Tare da Musu Addu'o'i
- Yayin da rikici ke kara ta'azzara tsakanin Isra'ila da Falasdinu, an fara samun rarrabuwan kai kan yakin
- Shugaban cocin RCCG, Fasto Adeboye ya bayyana cewa su na tare da Isra'ila a wannan halin yaki da su ke ciki kuma su na taya su addu'a
- Wannan martani na zuwa ne sa'o'i kadan bayan kungiyar CAN ta nemi kasashen biyu su koma teburin sulhu don samun zaman lafiya
Jihar Legas - Shugaban cocin RCCG, Fasto Enoch Adeboye ya ce su na tare kasar Isra'ila a wannan hali na yaki da su ke ciki.
Adeboye ya ce duk wani mamba na cocin a duniya na tare da kasar Isra'ila yayin da ta ke gwabza yaki da Falasdinu, Legit ta tattaro.
Meye Adeboye ya ce kan Isra'ila da Falasdinu?
Faston ya bayyana haka ne a jiya Laraba 11 ga watan Oktoba a faifan bidiyo da ya wallafa a shafin Twitter.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce a matsayinsu na Kiristoci 'yan Najeriya su na ta ya Isra'ila addu'a na samun nasara.
Ya ce:
"Ya ku 'yan uwana 'yan Isra'ila, ku sani muna tare da ku, kuma mu na muku addu'a a cikin wannan hali da kuke ciki.
"Ubangiji shi kadai mai girma zai ba ku nasara a yakin da ku ke ciki."
Rikicin ya kara kamari ne yayin da Isra'ila ta kai harin ramuwar gayya kan Falasdinu bayan kungiyar Hamas ta kai farmaki na bazata da makamin roka.
Meye martanin CAN kan Isra'ila da Falasdinu?
Wannan sakon Fasto Adeboye na zuwa ne sa'o'i kadan bayan Kungiyar CAN ta nemi a yi sulhu tsakanin kasashen biyu, cewar Vanguard.
Shugaban kungiyar a Najeriya, Fasto Daniel Okoh ya ce ba sa goyon bayan duk wani mataki da zai jawo rasa rayuka a duniya ko daga wane bangare.
Matashi Ya Budu Asusun Banki Don Yaran da Zai Haifa Su 6, Ya Ajiye N2.4bn, Ya Fadi Abin da Zai Tara a Bidiyo
Isra'ila ta yi alkawarin bai wa Najeriya kariya a kasar
A wani labarin, kasar Isra'ila ta yi alkawarin kare 'yan Najeriya da ke kasar yayin da ake ci gaba da gwabza yaki.
Jakadan kasar Najeriya shi ya bayyana haka inda ya ce komai na iya faruwa a halin yanzu amma za su yi kokarin kare rayuka.
Asali: Legit.ng