Juyin Mulki: Tinubu Ya Kunyata Shugaban Kasar Nijar da Aka Nemi Ya Gana da Shi

Juyin Mulki: Tinubu Ya Kunyata Shugaban Kasar Nijar da Aka Nemi Ya Gana da Shi

  • Ana tunanin an bijirowa Bola Ahmed Tinubu da maganar zama da Shugaba Abdourahamane Tchiani
  • Shugaban kasar Najeriya bai amince ya gana da wadanda su ka kifar da gwamnatin kasar Nijar ba
  • Janar Tchiani bai iya samun karbuwa wajen ECOWAS bayan hambarar da mulkin Mohamed Bazoum ba

Abuja - Bola Ahmed Tinubu ya yi watsi da bukatar da gwamnatin sojojin Nijar ta gabatar da samun damar haduwa da shi.

Vanguard ta ce Janar Abdourahamane Tchiani ya nemi ya yi zama ido da ido da shugaban Najeriyan, amma bai yi nasara ba.

Hakan ya na cikin yunkurin da sabuwar gwamnatin sojin Nijar ta ke yi na samun karbuwa bayan ta hambarar da farar hula.

Shugabannin Najeriya
Shugabannin Najeriya Hoto: @KashimSM
Asali: Twitter

Tinubu ba zai yi na'am da soji a Nijar ba

Rahoton da aka fara samu daga Empowered Newswire ya ce Bola Ahmed Tinubu bai yarda ya hadu da Abdourahamane Tchiani ba.

Kara karanta wannan

Sanatoci 107 Sun Tsoma Baki a Lamarin Tinubu v Atiku, Su na Goyon Bayan Shugaban Kasa

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zama da sojan da ya yi wa mulkin farar hula fyade a jamhuriyyar Nijar zai zama tamkar Najeriya ta halatta gwamnatin sojin.

Shugaban na Najeriya ya na ganin duk wata zama da zai yi da sababbin shugabannin zai zama ya ci fuskar Mohammed Bazoum ne.

Zaman Tchiani-Tinubu bai yiwu ba

Wata majiya a ofishin jakadancin Nijar a majalisar dinkin duniya ta ce al’ummar musulmai su ka kara bijiro da wannan bukata.

A wajen taron majaliar dinkin duniya da ya halarta a Birnin New York ne aka nemi shugaba Tinubu ya sa labule da Janar Tchiani.

Kafin nan malaman addinin musulunci sun kawo maganar a wata haduwa a Abuja.

ECOWAS za ta ja da kasar Nijar

Idan labarin Leadership ta tabbata, Janar Tchiani ya nemi ayi masa hanyar yadda zai yi zama daga shi sai shugaban kungiyar ECOWAS.

Kara karanta wannan

Yanzu aka fara: Sanata ya ce mulkin Tinubu ya dace da Najeriya, ya fadi dalilai

A taron 24 ga Agusta, majiyar ta ce Mai girma Tinubu ya jaddada cewa ba zai yi zama da wata haramtaciyyar gwamnati a Afrika ba.

Duk abin da ake yi ECOWAS ba ta amince da juyin mulkin Nijar ba, wannan ne ra’ayin shugaban Najeriya da yake shugabantarta.

Tinubu ya hana a yaki Nijar

An rahoto Bola Ahmed Tinubu ya na cewa shi ya hana a yaki jamhuriyyar Nijar domin ECOWAS ta yi niyyar shiga kasar tun tuni.

Shugaban Najeriya ya ce kungiyar kasashen yammacin Afrikan ta shirya sojoji da za su dura Nijar amma ya hana abin ya kai ga barin wuta.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng