Kotu Ta Yanke Wa Dan Amurka Daurin Shekaru 2 Kan Taba Cinyar Wata Mata
- Kotu ta yanke hukuncin daurin shekaru biyu ga wani mutumi kan zargin zuwa hannu a cinyar wata mata
- Wanda ake zargin mai suna Mohammed Jawad Ansari ya taba matar ne yayin da ta ke bacci a cikin jirgi
- Alkalin kotun, Fernando Aenlle-Rocha ya ci tarar Ansari Dala dubu 40 bayan yanke hukuncin daurin shekaru biyu
Amurka - Wata kotu a Amurka ta tasa keyar magidanci zuwa gidan yari daurin shekaru biyu kan zargin taba cinyar wata.
Ana zargin mutumin da zargin zura hannu a siket din matar yayin da ta ke barci a cikin jirgin sama.
Meye ake zargin magidancin da aikatawa?
An yanke shari'ar ce a jiya Alhamis 5 ga watan Oktoba a kotun majistare a Amurka, cewar NBC News.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana zargin Mohammed Jawad Ansari mai shekaru 50 da zura hannunsa cikin fatarin matar wacce ke gefensa a cikin jirgin yayin bulaguro zuwa Los Angeles na Amurka.
Wannan aika-aika na mutumin ta firgitar da matar tare da farkar da ita inda ta kai kararsa wurin jami'an jirgin saman.
Bangaren ma su kara sun bayyana yunkurin Ansari a matsayin cin zarafin mata da keta haddinsu wanda ya faru a watan Faburairu na 2020.
An shafe kwanaki hudu ana tafka shari'ar amma wanda ake zargin bai amince da aikata laifin ba inda ya ce ba ta da hujjar hakan ta faru.
Wane hukunci kotun ta yanke wa Ansari?
Har ila yau, matar ta gabatar da hujjoji kala-kala kuma kwarara wadanda su ka tabbatar da hakan, Al Arbiyya English ta tattaro.
Daga bisani an yanke wa Ansari hukunci zuwa gidan yari bayan kotu ta amince da hujjojin wacce ke kara.
Alkalin kotun, Fernando Aenlle-Rocha ya ci taran Ansari Dala dubu 40 tare da daurin shekaru biyu.
Magidanci ya bukaci kotu ta raba aurensu
A wani labarin, wani magidanci ya roki kotu ta raba aurensa da matarsa da su ka shafe shekaru 22.
Kotun ta fada wa magidancin cewa ai tuntuni babu aure a tsakaninsu a shari'ance.
Abayomi Oreyemi ya kai kara kotun majistare da ke Ibadan babban birnin jihar Oyo don bi masa kadunsa a kotun.
Asali: Legit.ng