Hambararren Sojin Nijar, Bazoum Ya Maka Sojin Kasar A Kotun ECOWAS Kan Tauye Masa Hakki

Hambararren Sojin Nijar, Bazoum Ya Maka Sojin Kasar A Kotun ECOWAS Kan Tauye Masa Hakki

  • Mohamed Bazoum, wanda aka hambarar a kan mulki a Nijar ya fara daukar matakan kare kansa
  • Bazoum ya maka sojin Jamhuriyar Nijar a kotun ECOWAS don kwato masa hakkinsa da aka tauye na tsare shi da iyalansa
  • Ya kuma bukaci kotun ta yi la'akari da yadda aka tauyewa 'yan kasar damar gudanar da siyasa ba tare da tsangwama ba

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Yamai, Nijar - Hambararren shugaban Jamhuriyar Nijar, Mohamed Bazoum ya maka sojin kasar a kotun ECOWAS.

Bazoum ya dauki wannan matakin ne ganin yadda sojin su ka tauye masa hakki na ci gaba da tsare shi tare da iyalansa ba bisa ka'ida ba.

Bazoum ya maka sojin Nijar a kotun ECOWAS
Hambararren Sojin Nijar, Bazoum Ya Dauki Mataki Kan Sojin Kasar. Hoto: Bola Tinubu, Bazoum, Tchiani.
Asali: Twitter

Me Bazoum ke bukata wurin ECOWAS a Nijar?

Ya bukaci kotun ECOWAS ta kwato masa hakkinsa na walwala da 'yanci a matsayinsa na dan Adam da kuma matarsa Hadiza Mabrouk da dansa Salem.

Kara karanta wannan

Obasanjo Ya Fusata, Ya Dauki Mataki Mai Tsauri Kan Matarsa Da Ta Roki Sarakuna a Madadinsa

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Idan ba a mantaba a ranar 26 ga watan Yuli ne sojin Nijar su ka hambarar da Bazoum tare da tsare iyalansa tun a wancan lokaci.

Hakan ya biyo bayan zarginsa da su ke da rashin gudanar da mulki yadda ya dace a kasar, cewar TRT Africa.

Meye martanin ECOWAS ga Bazoum na Nijar?

Maitre Mohamed Seydou, wanda shi ne lauyan Bazoum ya bukaci kotun ta yi mai yiyuwa don tilasta sojin sakin Bazoum da iyalansa.

A cikin takardar karar, Bazoum ya bukaci kotun ta yi la'akari da yadda sojin su ka tauyewa 'yan kasar 'yancin gudanar da siyasa cikin lumana.

Har ila yau, ya bukaci kotun ta tilasta shugaban sojin bin doka da oda don sanin yadda zai gudanar da mulki ba tare da sabawa doka ba.

Har zuwa lokacin tattara wannan rahoto, ECOWAS ba ta saka ranar sauraran karar ba, GhanaWeb ta tattaro.

Kara karanta wannan

Hotuna Sun Bayyana Yayin da Ambaliyar Ruwa Ta Yi Barna a Lagas, NEMA Ta Yi Martani

Haka kuma, a bangaren sojin Nijar su ma ba su ce komai ba game da wannan korafi na Bazoum da ya ke yi a kansu.

Bazoum ya koka kan irin abincin da sojin Nijar ke ba shi

A wani labarin, Tsohon shugaban kasa, Bazoum ya bayyana irin wahalar da ya ke sha a komar sojoji.

Bazoum ya ce wata gayar shinkafa kawai ake ba shi ba tare da ko mai ba wanda hakan tauye hakki ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.