Girgizar Kasa Mai Karfin Gaske Ta Halaka Mutum 632 a Kasar Morocco
- An samu aukuwar iftila'in girgizar ƙasa mai ƙarfin gaske a yankin birnin Marrakesh na ƙasar Morocco
- Girgizar wacce ke da ƙarfin maki 6.8 ta auku ne a tsakar daren ranar Juma'a, 8 ga watan Satumban 2023
- Ma'aikatar harkokin cikin gidan ƙasar ta tabbatar da cewa adadin mutanen da suka rasu ya kai, 632 yayin da wasu mutum 380 suka samu raunika
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Marrakesh, Morocco - An samu girgizar ƙasa mai ƙarfin gaske a birnin Marrakesh na ƙasar Morocco, a tsakar daren ranar Juma'a, 8 ga watan Satumban 2023.
Mutanen da suka riga mu gidan gaskiya a sakamakon girgizar ƙasar ya ƙaru zuwa sama da mutum 632, rahoton Sky News ya tabbatar.
A cewar bayanai daga ma'aikatar harkokin cikin gida ta ƙasar, wasu mutum 329 sun samu raunika, inda mutum 51 ke cikin mawuyacin hali.
Ma’aikatar ta tabbatar da cewa girgizar ƙasar wacce ke da ƙarfin maki 6.8, ta yi ɓarna a yankunan Marrakesh, Al-Haouz, Azilal, Ouarzazate, Taroudant da kuma Chichaoua.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jama'a da dama sun tserewa gidajensu a cikin dare domin kuɓutar da rayukansu, yayin da ake cigaba da aikin ceto, cewar rahoton Aljazeera.
Girgizar ƙasar mai karfi wacce ta auku a Marrakesh, yankin da masu yawon buɗe ido ke yawan zuwa, ta kwashe kusan mintuna 10, sannan an ji motsi a wasu biranen ƙasar da suka haɗa da Rabat, Casablanca da kuma Essaouira.
Ba a taɓa girgizar ƙasa irinta ba a ƙasar
Wakilin jaridar Sky News yana cikin birnin Marrakesh lokacin da iftila'in girgizar ƙasar ya auku a daren na ranar Juma'a.
Ya bayyana cewa girgizar ƙasar ta zarce dukkanin waɗanda ya taɓa gani sun auku a Morocco, inda ba a cika samun iftila'in girgizar ƙasa ba.
"Tana da ƙarfi sosai, ban taɓa ganin wanu abu makamancinta ba, tana da matuƙar ƙarfi sosai." A cewarsa.
Ya kuma bayyana cewa wasu mutanen sun kwana a tituna saboda tsoron ka da gidajensu su ruguje.
An Samu Girgizar Kasa a Siriya Da Turkiyya
A wani labarin kuma, an sake samun wata sabuwar girgizar kasa da ta auku a iyakar kasashen Turkiyya da Siriya, kwanaki bayan afkuwar ta faro da mutane sama da 40,000 suka kwanta dama a kasashen biyu.
Girgizar kasar mai girman 6.4 ta daki yankin Hatau ne na kasar Turkiyya, wacce ta yi barna a makwanni biyu da suka gabata.
Asali: Legit.ng