Jerin Sunayen Shugabannin Afirika Da Sojoji Suka Hambarar Da Gwamnatinsu Cikin Shekara 3 Da Suka Wuce
Nahiyar Afirika na fuskantar yawaitar hamɓarar da gwamnatin fararen hula, inda sojoji ke cigaba da karɓe mulki.
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Ƙasar Gabon ta zama ta baya-bayan nan inda sojoji suka hamɓarar da gwamnati a ranar Laraba, 30 ga watan Agusta.
A cikin shekara uku da suka gabata sojoji sun hamɓarar da gwamnatocin fararen hula sau bakwai a nahiyar Afirika.
Legit.ng ta tattaro sunayen shugabannin ƙasar da aka hamɓarar.
Shugaba Ali Bongo
Juyin mulki ya ritsa da shugaban ƙasar Gabon a ranar 30 ga watan Agusta, lokacin da wasu sojoji suka sanar da ƙarɓe mulki a ƙasar.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Mutane a babban birnin ƙasar Gabon, Libreville, sun fito suna murnar hamɓarar da gwamnatin Ali Bongo. Hakan ya kawo ƙarshen sama da shekara 50 da ahalinsa suka yi suna mulkar ƙasar mai yawan mutane sama da miliyan biyu.
Bidiyon Halin da Hamɓararren Shugaban Ƙasar Gabon Ke Ciki Ya Bayyana, Ya Aike da Saƙo Mai Muhimmanci
Shugaba Mohamed Bazoum
Shugaban ƙasar na Jamhuriyar Nijar ya rasa muƙaminsa ne bayan shugaban dakarun tsaron fadar shugaban ƙasa, Janar Abdourahamane Tchiani, ya hamɓarar da gwamnatinsa a ranar 26 ga watan Yulin 2023.
Shugaba Roch Marc Christian Kaboré
Sojoji sun hamɓarar da gwamnatin shugaban ƙasar Burkina Faso bisa umarnin Paul-Henri Sandaogo Damiba, wanda ya karɓe ikon sansanin sojojin ƙasar a ranar 23 ga watan Janairun 2023.
Sojojin sun yi nuni da cewa taɓarɓarewar tsaro da ƙarin ayyukan ƴan ta'adda, su ne dalilan da suka sanya suka hamɓarar da gwamnatin.
Haka kuma watanni tara bayan hamɓarar da gwamnatin Shugaba Kabore, wasu sojoji sun ƙara yin juyin mulki a ƙasar.
Shugaba Omar al-Bashir
Janar Abdel Fattah al-Burhan ya hamɓarar da gwamnatin shugaban ƙasar Sudan, Omar al-Bashir a shekarar 2019.
Tun daga wannan juyin mulkin har yanzu ƙasar ta kasa samun zaman lafiya.
Shugaba Alpha Condé
Mamady Doumbouya ya sace shugaban ƙasar Guinea mai shekara 83 a watan Satumban 2023, bayan shugaban ƙasar ya sauya kundin tsarin mulkin ƙasar ta yadda zai cigaba da mulki a karo na uku.
Tun daga wannan lokacin Doumbouya ya ƙi mayar da mulki hannun farar hula, inda ya dakatar da amfani da kundin tsarin mulki.
Shugaba Ibrahim Boubacar Keïta
Sojoji sun hamɓarar da gwamnatinsa a shekarar 2020 bayan hargitsin da ya biyo bayan zaɓen ƴan majalisar ƙasar na watan Maris da Afirilu, da sace shugaban ƴan adawar ƙasar Soumaila Cissé.
Tun daga wannan lokacin ƙasar ta shiga cikin rigingimun siyasa inda aka ƙara yin wani juyin mulkin a watan Mayun 2021.
Shugaba Idriss Déby
Shugaban ƙasar na Chadi ya rasa ransa a hannun ƴan tawayen ƙasar a ranar 20 ga watan Afirilun 2021. Deby ya hau kan mulki ne bayan ya yi juyin mulki a shekarar 1999.
A yayin da wa'adin shekara 30 na mulkin Deby ya ƙare, har yanzu ƙasar ba ta koma kan turbar dimokuraɗiyya ba inda sojoji su ke cigaba da jagorantar ƙasar.
Kasashen Rwanda Da Kamaru Sun Firgita
A wani labarin kuma, ƙasashen Rwanda da Kamaru sun yi garambawul kan rundunar tsaron ƙasashensu.
Garambawul ɗin na zuwa ne bayan sojoji sun hamɓarar da gwamnatin Shugaba Ali Bongo na ƙasar Gabon.
Asali: Legit.ng