Yadda Likitoci Suka Gano Tana Mai Rai A Kwakwalwar Wata Mata
- Likitoci sun gano tana mai rai a kwakwalwar wata tsohuwa mai shekaru 62 a kasar Australia
- Tsayin tanan da aka gano ya kai inci uku kuma wannan ne karo na farko da ake samun irin haka
- Masana kimiya sun ce watakila tanar ta shiga jikin matar ne a lokacin da take tsintar ganye a bakin kogi da ke gaban gidanta
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Wata kwararriyar likitar kwakwalwa, Dr Hari Priya Bandi, ta yi wa wata mata yar kasar Austalia mai shekaru 64 tiyata a kwakwalwa, inda ta yi gamo da abun da bata taba tsammani ba.
Dr Bandi ta fitar da wata tana mai rai wacce tsayinta ya kai santimita takwas wato inci 3 tana wulgawa a tsakanin almakashinta.
Wannan shine karo na farko da ake gano tana mai rai a cikin kwakwalwar dan adam, jaridar Daily Trust ta rahoto.
Bandi ta sanar da CNN cewa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Na taba gamuwa da tanaye ne kawai ta hanyar amfani da basirar aikin lambuna mara kyau...Ina tsoronsu kuma wannan ba abu da na saba da shi bane ko kadan."
Sakamakon binciken masana kan tanar da aka gano a kwakwalwar matar
Abun da aka gano ya sa an shiga binciken gaggawa don gano wacce irin cuta ce, masanin cututtuka masu yaduwa a asibitin Canberra, Sanjaya Senanayake ya fada wa CNN.
Wani abokin aiki a dakin gwaje-gwaje na asibitin ya sami damar isa ga wani kwararren masanin kwayoyin cututtuka a wata hukumar binciken kimiyya ta gwamnati sannan ya samu amsar da basu yi tsammani ba.
Senanayake ya ce:
"Mun yi nasarar aika masa da tanar mai rai, kuma ya yi nasarar duba ta sannan kuma nan take ya gane ta."
Gwaje-gwajen kwayoyin halitta sun tabbatar da cewa 'Ophidascaris Robertsi' ce, wata tana da a kan samu a jikin manyan macizai, a cewar wata sanarwa daga Jami'ar Australia da Asibitin Canberra.
"A iya saninmu, wannan shine karo na farko da ake samun irin haka a kwakwalar dan adam," inji Senanayeka, wanda ya kasance Farfesa a Jami'ar Australia.
Masana kimiya sun ce babu mamaki tanar ta shiga jikin matar ne a lokacin da take tsintar ganye a kusa da bakin kogin da ke gaban gidanta.
Likitoci da masana da ke kan lamarin matar sun ce suna zargin matar ta gamu da wannan cuta ne bayan ta yi amfani da ganyayyakin da tana ko wanda kwaya-kwayan tanar ke makale wajen girka abinci.
Yadda aka gano tana a kwakwalwar tsohuwa mai shekaru 62
An fara kwantar da matar a wani asibiti a karshen watan Janairun 2021 bayan ta yi fama da ciwon ciki da gudawa na tsawon makonni uku, sai kuma tari, zazzabi da yawan gumin dare suka biyo baya.
Yan watanni bayan nan, matar ta shiga yanayi na mantuwa da damuwa sannan aka tura ta wani asibiti a babban birnin Austaralia, hoton kanta da aka dauka ya nuna cewa akwai wani abu makale a bangaren kwakwalwarta ta gaba.
Dan Najeriya ya fallasa tulin zinare a Zamfara, ya saki bidiyo
A wani labari na daban, Mahdi Shehu, mai sharhi kan al'amuran jama'a ya fallasa wani haramtaccen wurin hakar zinare a wani kauye a jihar Zamfara.
Mai rajjin kare hakkin dan adam din ya kuma saki wani faifan bidiyo da ke nuna ma'aikatan da ke aikin hakar zinare a yayin da ya yi karin haske kan mamalakinsa.
Asali: Legit.ng