Juyin Mulkin Nijar: Sojoji Sun Yi Bayanin Yadda Dawo Da Bazoum Kan Mulki Ba Zai Yiwu Ba

Juyin Mulkin Nijar: Sojoji Sun Yi Bayanin Yadda Dawo Da Bazoum Kan Mulki Ba Zai Yiwu Ba

  • Shugabannin sojojin juyin mulkin Nijar sun bayyana cewa hamɓararren shugaba Bazoum ba zai dawo kan mulki ba
  • Janar Abdulsalami Abubakar, ɗaya daga cikin jagororin wakilan ECOWAS shi ne ya bayyana haka bayan ya gana da Firaminista Ali Mahaman Lamine Zeine
  • A halkn da ake ciki ƙoƙarin da ECOWAS ke yi na warware rikicin bai haifar da wani ɗa mai ido bayan sojojin sun ƙeƙashe ƙasa kan ƙin barin mulki

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Janar Abdulsalami Abubakar wanda ya jagoranci tawagar wakilan ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS), ya bayyana yadda tattaunawarsu ta kaya da sojojin juyin mulkin Jamhuriyar Nijar.

Kamar yadda @Imranmuhdz ya sanya a X (wacce a baya a ka sani da Twitter), Janar Abdulsalam a yayin ganawarsa da sojojin, sun gaya masa cewa babu batun dawo da Shugaba Mohamed Bazoum a kan mulki.

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Nijar: Shugaba Tinubu Ya Tarbi Wakilan Amurka, Ya Bayyana Sabbin Bayanai Kan Matsayar ECOWAS

Sojojin Nijar sun ce ba za su ba Bazoum mulki ba
Janar Abdulsalam tare da Ali Mahamine Zeine
Asali: Twitter

Shugaba Bazoum ba zai dawo kan mulki ba

A kalamansa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Ya bayyana cewa juyin mulki ya riga da ya faru sannan an hamɓarar da Shugaba Bazoum. Domin haka maganar dawo da shi kan mulki ba abu ba ne mai yiwuwa."
"Ya buƙaci ECOWAS ta mayar da hankali kan abubuwan da za su amfani al'ummar Nijar sannan su ƙyale batun dawo da Bazoum kan mulki. Ya haƙiƙance cewa za su tattauna kowane abu ba tare da matsala ba, amma ban da maganar dawo da shi kan mulki saboda hakan ba zai yiwu ba."

Da yake cigaba da bayaninsa, tsohon shugaban mulkin soja na Najeriya, a wata Hira da BBC News Africa, ya bayyana cewa sojojin sun yi nuni da cewa zai ɗauki aƙalla shekara uku kafin su dawo da ƙasar kan turbar mulkin dimokuraɗiyya..

Kara karanta wannan

An Kuma Yin Juyin Mulki a Wata Kasar Afrika Ta Yamma Ta Daban? Bayanai Sun Fito

Janar AbdulSalami ya bayyana cewa:

"Gwara yanzu ma da su ke yin magana ba kamar a farko ba inda suka ƙi cewa komai ko bayar da damar da za a tattauna."
"Sai dai, batun sai nan da shekara uku za su mayar da ƙasar kan turbar dimokuraɗiyya, na cikin rahoton da muka gabatarwa Shugaba Tinubu kan tattaunawar da muka yi da su."

Tinubu Ya Bayyana Matsayar ECOWAS

A wani labarin kuma, shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana matsayar ƙungiyar ECOWAS kan rikicin Jamhuriyar Nijar.

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa yaƙi ba abun so ba ne amma ƙungiyar za ta tabbatar cewa ta kare dimokuraɗiyya a ƙasar ta Nijar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng