Nijar Ta Ƙulla Ƙawance Na Soji Da Kasashen Burkina Faso Da Mali Domin Tunkarar ECOWAS

Nijar Ta Ƙulla Ƙawance Na Soji Da Kasashen Burkina Faso Da Mali Domin Tunkarar ECOWAS

  • Shugaban mulkin soji na Nijar, Abdourahmane Tchiani, ya ƙulla ƙawance na soji tsakanin Nijar, Mali da Burkina Faso
  • Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da ƙungiyar ECOWAS ke duba yiwuwar yin amfani da ƙarfi wajen dawo da dimokuraɗiyya a ƙasar
  • Yarjejeniyar ta bai wa ƙasashen damar taimakawa Nijar a duk sanda aka kawo ma ta hari

Niamey, Nijar - Shugabannin juyin mulkin jamhuriyar Nijar, sun ƙulla ƙawance na soji da ƙasashen Burkina Faso da Mali, waɗanda su ma suna ƙarƙashin mulkin soji.

Wakilan ƙasashen uku ne suka fitar da wannan sanarwar ranar Alhamis ɗin da ta gabata a Niamey babban birnin ƙasar kamar yadda DW ta ruwaito.

Nijar ta shiga wata yarjejeniya ta soji da Mali da Burkina Faso
Nijar ta ƙulla ƙawance na soji da ƙasashen Mali da Burkina Faso. Hoto: Islam Channel
Asali: UGC

Me ƙawancen sojin Nijar, Mali da Burkina Faso ke nufi?

Wannan ƙawance na soji da aka ƙulla tsakanin ƙasashen uku na nufin za su iya taimakawa juna a yayin da aka kawo musu hari ko a wata matsala da ta shafi tsaro.

Kara karanta wannan

An Kuma Yin Juyin Mulki a Wata Kasar Afrika Ta Yamma Ta Daban? Bayanai Sun Fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdourahmane Tchiani ya bai wa ƙasashen na Mali da Burkina Faso damar kawo ma sa ɗauki da zarar ƙungiyar ECOWAS ko wata ƙasa ta kawowa Nijar hari.

Haka nan kuma yarjejeniyar da suka ƙulla, za ta samar da wani aiki na haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen uku wajen yaƙi da 'yan ta'addan da suka damesu kamar yadda Reuters ta wallafa.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da abubuwa suke ƙara kankama, kan yiwuwar amfani da ƙarfin soji wajen dawo da dimokuraɗiyya a Nijar da ECOWAS ke shirin yi.

An samu ƙarancin shanu da sauran kayayyaki saboda rufe iyakoki

A baya Legit.ng ta kawo rahoto kan yadda al'umma musamman ma waɗanda ke kasuwanci a jihohin da suka haɗa iyakoki da Nijar suke kokawa.

Wasu daga cikin 'yan kasuwar sun koka kan ƙarancin dabbobi da sauran kayayyaki da ake samu tun bayan rufe iyakokin Najeriya da Nijar da aka yi a kwanakin baya.

Kara karanta wannan

Nijar: Algeria Da Egypt Sun Fadi Matakin Da Ya Kamata a Dauka Kan Sojojin Juyin Mulki

Hakan a cewar da dama daga cikin 'yan kasuwar, yana ci gaba da janyo mu su asara ta miliyoyin nairori a kowace rana.

Sojojin Nijar sun ce ba za su mayar da Bazoum kan mulki ba

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan bayanin da sojojin juyin mulkin jamhuriyar Nijar suka yi a yayin zantawarsu da Janar Abdulsalami Abubakar mai ritaya.

Sun ce ba za su mayar da hamɓararren shugaban ƙasar wato Mohammed Bazoum kan kujerarsa ba, amma a shirye suke su tattauna wani abun daban.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng