Sojojin Juyin Mulkin Nijar Sun Ce Ba Za Su Mayar Da Bazoum Kan Mulki Ba, Abdulsalami Abubakar

Sojojin Juyin Mulkin Nijar Sun Ce Ba Za Su Mayar Da Bazoum Kan Mulki Ba, Abdulsalami Abubakar

  • Sojojin juyin mulkin Nijar sun ce batun dawo da Bazoum kan mulki ba abu ba ne mai yiwuwa
  • Sun ce a shirye suke su tattauna a kan komai amma banda batun mayar da mulki ga Bazoum
  • Sun bayyana hakan ne a yayin tattaunawarsu da Abdulsalami Abubakar da Sarkin Musulmi

FCT, Abuja - Jagoran masu shiga tsakani na ECOWAS kan rikicin jamhuriyar Nijar, Abdulsalami Abubakar, ya ce sojojin juyin mulkin Nijar sun ce ba za su maida Bazoum kan mulki ba.

Ya bayyana hakan ne a zantawarsa da sashen Hausa na BBC kwanaki kaɗan bayan dawowarsu daga jamhuriyar Nijar wajen sasanci.

Sojojin Nijar sun ce ba za su maida Bazoum kan kujerarsa ba
Sojojin juyin mulkin Nijar sun ce ba za su mayarwa da Bazoum mulki ba. Hoto: @BashirAhmaad
Asali: Twitter

Ba zai yiwu sojojin Nijar su maidawa Bazoum mulki ba

Abdulsalami Abubakar ya ce shugaban sojojin wato Abdourahmane Tchiani a yayin da suka gana da shi, ya bayyana mu su cewa tunda sun riga da sun kifar da gwamnatin Bazoum, babu maganar mayar da shi kan kujera.

Kara karanta wannan

"Akwai Haske": Abdulsalami Ya Yi Magana Kan Tattaunawarsu Da Sojojin Juyin Mulkin Nijar

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce sojojin sun ba da tabbacin cewa a shirye suke su tattauna a kan komai amma banda batun mayarwa da tsohon shugaban ƙasar mulkinsa da suka riga suka karɓe.

Ya ƙara da cewa bayan shafe aƙalla sa'o'i uku suna tattaunawa da shugabannin juyin mulkin, sun kuma samu damar ganawa da hamɓararren shugaban ƙasar Mohamed Bazoum.

Abinda sojojin juyin mulkin suke so a yi mu su

Abdulsalami Abubakar ya kuma bayyana cewa daga cikin sharuɗan sulhun da sojojin suka gindaya akwai buƙatar a ɓude mu su iyakokin Najeriya domin abinci da magunguna su riƙa shiga ƙasar.

Sojojin sun kuma buƙaci Najeriya ta mayarwa da jamhuriyar Nijar wutar lantarkinta da ta datse tun a farko-farkon takun saƙar.

Sojojin sun ce ko da a yanayi na yaƙi ana barin magunguna da abinci su shiga ƙasa, ballantana yanzu ba yaƙi ake yi ba.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu Ya Shiga Ganawar Sirri da Ribadu, Abdussalami kan Yakin ECOWAS a Nijar

Abdulsalami ya kuma bayyana cewa sojojin sun yankewa Mohamed Bazoum wutar lantarki, inda suka ce ba za su mayar ma sa da ita ba har sai Najeriya ta mayarwa da Nijar wuta.

Dakta Gumi ya buƙaci a mayarwa da Nijar wutar lantarki

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan tsokacin da fitaccen malamin nan Dakta Ahmad Abubakar Mahmud Gumi ya yi dangane da juyin mulkin jamhuriyar Nijar.

Dakta Gumi ya ce wajen Shugaba Bola Tinubu ya kamata malamai da sarakuna su je domin faɗa ma sa ya mayarwa da Nijar wutar lantarki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng