Juyin Mulki: Bayanai Sun Fito Kan Batun Ƙasar Aljeriya Na Ba Nijar Wutar Lantarki Kyauta

Juyin Mulki: Bayanai Sun Fito Kan Batun Ƙasar Aljeriya Na Ba Nijar Wutar Lantarki Kyauta

  • Batun da Adamu Garba ya yi na cewa gwamnatin Aljeriya ta shirya ba Nijar wutar lantarki kyauta, ƙarya ne
  • Hakan ya faru ne saboda babu daga cikin sojojin juyin mulkin Nijar da gwamnatin Aljeriya, da suka fito suka tabbatar da hakan
  • Wannan ƙaryar da aka ƙirƙiro ka iya kawo saɓa dangantakar diflomasiyya a tsakanin ƙasashen

Yamai, Nijar - Iƙirarin da Adamu Garba, wani jigo a jam'iyyar All Progressives Congress (APC), ya yi a shafinsa na Facebook cewa ƙasar Aljeriya, ta shirya ba Nijar wutar lantarki kyauta, ƙarya ne.

Bincike ya nuna cewa batun na shi babu gaskiya a ciki saboba babu daga cikin gwamnatin sojojin Nijar da gwamnatin ƙasar Aljeriya, da suka fito suka tabbatar da hakan.

Aljeriya ba ta ba Nijar wutar lantarki kyauta
Ba gaskiya ba ne batun Aljeriya n ba Nijar wutar lantarki Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: UGC

Haka kuma babu wata kafar watsa labarai da ta rahoto hakan.

Kara karanta wannan

Wata Sabuwa: An Bankado Wani Sabon Tuggu Da Tinubu Ke Shiryawa a Kan Atiku Abubakar

ECOWAS ta matsa lamba kan gwamnatin sojojin Nijar

A ranar 26 ga watan Yuli, dakarun sojojin da ke tsaron fadar shugaban ƙasa, a ƙarƙashin jagorancin Janar Abdourahamane Tchiani, suka hamɓarar da gwamnatin Shugaba Mohamed Bazoum.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hakan ya sanya ƙungiyar ECOWAS ta ƙaƙaba takunkumi kan ƙasar, waɗanda suka haɗa da kulle iyakokin ƙasar, yanke tallafin da Nijar ke samu, da kulle asusun duk masu goyon bayan juyin mulkin.

Shugaba Bola Tinubu na Najeriya ya ƙara matsa lamba ta hanyar yanke wutar lantarkin da Najeriya ke ba Nijar a ranar 3 ga watan Agusta, inda ya buƙaci lallai sai an dawo da mulkin dimokuraɗiyya a ƙasar.

Bayanan da suka fito a ƴan kwanakin nan sun nuna cewa Najeriya na bin Nijar bashin $5.48m (N4.22bn) na kuɗin lantarki.

Sai dai, yana da kyau a sani cewa gwamnatin Aljeriya ba ta son ECOWAS ta yi amfani da ƙarfin soja a Nijar, yayin da ta kuma yi Allah wadai da juyin mulkin da aka yi a ƙasar.

Kara karanta wannan

Abdourahmane Tchiani Ya Fadi Matakin Da Za Su Dauka Idan ECOWAS Ta Kawowa Nijar Hari

Batun Adamu Garba ba gaskiya ba ne

Saboda haka, batun da Adamu Garba, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, ya yi babu gaskiya a cikinsa, sannan zai iya kawo saɓa dangantakar diflomasiyya da ke a tsakanin ƙasashen.

A lokacin haɗa wannan rahoton, rubutun da ya yi a Facebook ya samu sharhi 65 sannan mutum 15 sun sake watsa shi.

ECOWAS ta yi fatali da matsayar sojojin Nijar

A wani labarin kuma, ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS), ta yi fatali da matsayar sojojin da suka yi juyin mulkin a Nijar ta shafe shekara uku a kan mulki.

Ƙungiyar ta nuna rashin amincewarta kan wannan shirin na sojojin juyin mulkin, inda ta ce sam hakan ba abin da za ta yarda da shi ba ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng