Kuskure a Banki Ya Sanya Mutane Sun Yi Ta Cirar Kudi Kyauta a ATM
- Wani kuskuren IT a bangaren harkokin bankuna a ƙasar Ireland ya sanya kwastomomin da ba su da kuɗi a asusu sun je ATM sun cire kusan N833k
- Bidiyoyin da ke yawo a soshiyal midiya sun nuna masu asusu a banki suna layin cirar kuɗi ko da kuwa ba ko sisi a asusun su
- A yayin da mutanen su ke tunanin sun ci bulus, bankin ya yi gargaɗin cewa zai cire kuɗin daga asusun su
Wani babban kuskure a ɓangaren IT ya ba masu ajiya a banki waɗanda ba su da kuɗi a asusun su damar cirar kuɗi har N833k daga bankin Ireland.
Kuskuren IT ɗin ya auku ne a manhajar bankin, wanda hakan ya sanya mutane yin ribubin neman cin bulus, cewar rahoton The sun.
Bidiyoyin da aka sanya a soshiyal midiya sun nuna mutane da dama a layin ATM suna jiran su cira kuɗi.
Haka kuma, kwastomomin da ba su da kuɗi ko kuɗin su ba su da yawa a asusu, za su iya tura kusan €1000, wanda yake matsayin kusan N833k.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Bankin Ireland ya aike da gargadi
Bankin Ireland ya gargaɗi masu cirar kuɗin waɗanda babu kuɗi a asusun su cewa zai dawo da kuɗaɗen da suka cire.
Kamar yadda The Telegraph ta rahoto, bankin ya bayyana cewa:
"Muna son tunatar da mutane cewa idan suka tura kuɗi ko cire kuɗi, ciki har abin da ya wuce ƙa'ida, za mu cire waɗannan kuɗaɗen daga asusun su."
Bankin ya bayyana cewa yana aiki tuƙuru wajen magance matsalar da ake fuskanta wajen tura kuɗi ta hanyar amfani da manhajar bankin.
"Muna sane da cewa masu amfani da manhajar bankin mu da 365Online na fuskantar matsaloli."
"Muna aiki tuƙuru domin gyara matsalar sannna muna bayar da haƙuri kan akasin da aka samu."
A wani bidiyo da Chris Rattigan ya sanya a Twitter, ya nuna mutanen akan layin ATM. Wasu sun bayar da shawarar a kulle ATM ɗin.
Tashin Dala Ya Ritsa Da Daliban Najeriya a Kasar Waje
A wani labarin kuma, ɗalibai ƴan Najeriya sun koka kan yadda tashin dala yake shafar karatunsu a ƙasar waje.
Daliban sun nemi gwamnati da ta kawo musu agaji kada karatun da su ke yi a ƙasashen waje ya samu tangarɗa.
Asali: Legit.ng