Jerin Juyin Mulkin da Sojoji Suka Taba Yi Tun 1974 Zuwa 2023 a Jamhuriyyar Nijar
- A watan Yulin 2023, sojojin Nijar su ka hambarar da gwamnatin Mohammed Bazoum na farar hula
- Kafin yanzu, dakarun sojoji sun yi nasarar kifar da shugabanni sau hudu a tarihin Jamhuriyyar Nijar
- A 1974 aka bude tarihin juyin mulki, aka kifar da gwamnatin shugaban kasar farko, Hamani Diori
Aljazeera ta tattaro gajeren tarihin juyin mulkin da aka yi wa shugabannin Nijar a kusan tsawon shekaru 50.
1. 1974
A Afrilun 1974, Laftanan Kanal Seyni Kountche ya kawo karshen shekaru 14 da Hamani Diori ya yi a kan mulki, ya kuma ruguza majalisar tarayyar Nijar.
Rahoton ya ce ana zargin Kanal Diori ya hallaka mutane 20 wajen kafa gwamnatin soja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
2. 1996
Sai bayan fiye da shekaru 20 aka sake samun sojojin da su ka kifar da Shugaban kasa Mahamane Ousmane da Fira Ministansa Hama Amadou a farkon 1996.
Shugaban hafsun sojojin lokacin, Laftanan Kanal Ibrahim Bare Mainassara ya karbi ragama.
3. 1999
Da wasu sojojin tawaye su ka kashe Ibrahim Bare Mainassara a filin jirgi a Niamey, sai aka samu juyin mulki na uku a tarihin Nijar, an yi hakan ne a 1999.
Shugaban sojojin fadar shugaban kasa, Daouda Malam Wanke ya karbi mulki da niyyar yin zabe.
4. 2010
A shekarar 2010 ne aka samu wasu sojoji a karkashin inuwar CSDR su ka yi waje da shugaba Tandja da ministocinsa, su ka dakatar da kundin tsarin mulki.
Bayan rusa majalisa, Janar Salou Djibo ya shirya zaben da Mahamadou Issoufou ya lashe a 2011.
4. 2023
Abdulrahman Tchiani ya jagoranci tawaye a Niamey, aka tsare Mohammed Bazoum a fadar shugaban kasa, bayan lokaci kadan aka sanar da canjin iko.
Janar Tchiani ya karbi gwamnati da karfi da yaji, hakan ya bar al’ummar nahiyar a a dar-dar.
Wani halin ake ciki a Nijar?
Juyin Mulkin Nijar: Da Gaske Janar Tchiani Ya Kira Gwamnatin Tinubu Da haramtacciya? Gaskiya Ta Yi Halinta
Wani mazaunin Nijar ya fada mana sun ji dadin yadda mutanen Najeriya su ke taimaka masu da addu’o’i, ya ce sun soma hango alamun zaman lafiya.
Wata da ke zaune a makwabtan ta ce Nijarawa sun ga tasirin addu’o’in da ake yi domin gudun rikici ya barke tsakanin kasashen ECOWAS da jamhuriyyar.
A cewar wani mazaunin garin Maradi da mu ka sakaya sunansa, abubuwa su na lafawa:
“Nijar a halin yanzu da-dama. Masallatai da makarantun addinin musulunci sai addu’o’i ake yi na Allah (SWT) ya dawo mana da kwanciyar hankali, ya kuma ba mu mafita.”
- Wani mazauni
Shawarar Dambazau ga Najeriya
Kwanaki aka ji Janar Abdulrahman Bello Dambazau (Mai ritaya) ya ce kifar da gwamnati da aka yi a Nijar yana da tasiri ga tsaro da tattalin Najeriya.
Tsohon hafsun sojojin kasar Najeriyan ya nuna za a iya fama da matsalar ‘yan gudun hijira ganin halin da ake ciki yau a Benin, Nijar, Chad da kuma Kamaru.
Asali: Legit.ng