Nijar Za Ta Tsallake Takunkuman Da ECOWAS Ta Kakaba Ma Ta, In Ji Firaministan Nijar Lamine Zeine

Nijar Za Ta Tsallake Takunkuman Da ECOWAS Ta Kakaba Ma Ta, In Ji Firaministan Nijar Lamine Zeine

  • Firaministan Nijar, Ali Mahaman Lamine Zeine, ya bayyana cewa ƙasarsa za ta haye duk takunkuman da aka sanya ma ta
  • Ya bayyana hakan ne a cikin wata tattaunawa da aka yi da shi, wacce aka wallafa ranar Litinin
  • Zeine ya ce a shirye suke su tattauna da ECOWAS wajen ganin an samu daidaito a tsakani

Niamey, Nijar - Sabon Firaministan jamhuriyar Nijar, Ali Mahaman Lamine Zeine, ya bayyana cewa jamhuriyar Nijar za ta jure duk takunkuman da ECOWAS ta sanya ma ta.

Ya bayyana hakan ne a wata tattaunawa da gidan talabijin na France 24 ya wallafa a shafinsa na yanar gizo ranar Litinin.

Zeine ya ce Nijar za ta jure duk takunkuman da aka sanya ma ta
Lamine Zeine ya ce Nijar za ta tsallake duk takunkuman da ECOWAS ta sanya ma ta. Hoto: Sadiq Mohammed
Asali: Facebook

ECOWAS ta sanyawa Nijar takunkumi bayan juyin mulki

Kungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), ta sanar da sanya takunkumai kan jamhuriyar Nijar biyo bayan juyin mulkin da sojojin ƙasar suka yi.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Malaman Izala sun dira Nijar don neman hanyar sulhu a batun juyin mulki

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Takunkuman da ECOWAS ta sanyawa Nijar sun haɗa da dakatar da hulɗar kasuwanci, katse wutar lantarki, da kuma rufe iyakokin Najeriya da Nijar.

Shugabannin mulkin soji na Nijar sun bayyana cewa takunkuman da aka sanya ba kan ƙa'ida suke ba kuma ba su dace ba duba da irin halin da suka jefa 'yan ƙasashen biyu.

Muna son ci gaba da kiyaye alaƙar da ke tsakanin Najeriya da Nijar

Zeine ya nuna ƙwarin gwiwarsa kan zuwan da wakilan ECOWAS suka yi a ƙarshen makon nan, wanda hakan ke nuna alamar buɗe ƙofar tattaunawa kamar yadda Vanguard ta wallafa.

Ya bayyana cewa suna da burin ganin sun kiyaye daɗaɗɗiyar alaƙa da ke tsakanin Najeriya da Nijar, sannan kuma ya nemi ECOWAS ta fi mayar da hankali wajen gyara tattalin arziƙin ƙasashenta.

Kara karanta wannan

Turo soji su yaki Nijar: 'Yan wata jihar Arewa a Najeriya sun fara zanga-zangar adawa da ECOWAS

Ya tabbatarwa da ɗaukacin al'ummar ƙasar Nijar cewa gwamnatinsu za ta yi iya bakin ƙoƙarinta wajen ganin ta yi wa 'yan ƙasar abinda suke so.

Tchiani ya amince zai tattauna da ECOWAS

Legit.ng a baya ta yi rahoto kan amincewar da shugaban juyin mulkin jamhuriyar Nijar, janar Abdourahmane Tchiani ya yi na ba da ƙofar tattaunawa tsakaninsa da ECOWAS.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da abubuwa ke ƙara ɗaukar zafi ta yanda ake fargabar ɓarkewar yaƙi tsakanin Nijar da dakarun ECOWAS.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng