Sojojin Juyin Mulkin Nijar Za Su Tuhumi Hambararren Shugaba Bazoum

Sojojin Juyin Mulkin Nijar Za Su Tuhumi Hambararren Shugaba Bazoum

  • Sojojin da suka hamɓarar da gwamnatin tsohon Shugaba Mohamed Bazoum za su tuhume shi a gaban kotu
  • Sojojin juyin mulkin suna zargin tsohon shugaban ƙasar da cin amanar ƙasa da riƙon sakainar kashi kan tsaron ƙasar
  • Shugaba Mohamed Bazoum dai ya kasance yana tsare a hannun sojojin tun bayan da suka kifar da gwamnatinsa

Jamhuriyar Nijar - Shugabannin juyin mulkin Jamhuriyar Nijar, sun tabbatar da aniyarsu ta tuhumar hamɓararren tsohon shugaban ƙasa Mohamed Bazoum.

Sojojin za su tuhumi tsohon shugaban ƙasar ne bisa zargin cin amanar ƙasa a gaban manyan kotunan duniya.

Sojoji juyin mulkin Nijar za su tuhumi Bazoum
Shugaba Bazoum zai fuskanci tuhuma a kotu Hoto: Mohamed Bazoum
Asali: Twitter

Mohamed Bazoum mai shekara 63 a duniya, ya kasance dai a tsare a hannun sojojin tun bayan da aka kifar da gwamnatinsa a ranar 26 ga watan Yulin 2023.

Zagazola Makama ya rahoto cewa hakan dai na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin CNSP, Amadou Abdramane ya fitar a gidan talbijin na ƙasar, a ranar Lahadi, 13 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Ya ake ciki? An fadi yanayin da Bazoum ke ciki bayan ganawarsa da likitansa

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Kakakin na CNSP ya musanta zargin da ɗiyar tsohon shugaban ƙasar ta yi na cewa sojojin sun hana Shugaba Mohamed Bazoum abinci da ganin likitansa.

A cikin sanarwar Abdramane ya bayyana cewa an bar likitoci sun duba Bazoum inda suka tabbatar da cewa baya fama da wata rashin lafiya, cewar rahoton The Cable.

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Ya zuwa yanzu gwamnatin Nijar ta tattaro dukkanin hujjojin da ake buƙata domin tuhumar hamɓararren shugaban ƙasa da ƙawayensa na gida da waje kan cin amanar ƙasa da yin wasa da tsaron Jamhuriyar Nijar."

Sun koka kan takunkumin ECOWAS

Sojojin sun bayyana cewa takunkumin da ECOWAS ta ƙaƙaba kan ƙasar ya sanya jama'a na shan wahala wajen samun magunguna, abinci da wutar lantarki.

Sojojin sun bayyana cewa a shirye su ke domin ba ƴan Nijar dukkanin taimakon da ya dace domin tsamo su daga cikin halin da sanya takunkumin ya jefa su a ciki.

Kara karanta wannan

Daga karshe: Malaman Izala sun dira Nijar don neman hanyar sulhu a batun juyin mulki

Sai dai, sojojin sun tabbatar da cewa a shirye su ke su mayar da martani kan kowane farmaki da za a iya kai musu.

Matakan ECOWAS Da Suka Janyo Barazana Ga Bazoum

A baya kun ji cewa wasu daga cikin matakan da ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS) ta ɗauka sun janyo barazana ga rayuwar Bazoum.

Matakan da ƙungiyar ta ɗauka akan sojojin ya fusata su inda suka yi barazanar halaka hamɓararren tsohon shugaban ƙasar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng