Idan Dakarun ECOWAS Suka Shigo Da Yaki, Sojojin Nijar Za Su ‘Kashe’ Bazoum

Idan Dakarun ECOWAS Suka Shigo Da Yaki, Sojojin Nijar Za Su ‘Kashe’ Bazoum

  • Sojojin kasar Nijar za su iya maida Mohammed Bazoum ya zama gawa idan ba ayi hattara ba
  • ‘Yan tawayen da su ka karbi mulki sun nuna muddin aka auko masu da yaki, ba za a ji da dadi ba
  • Sojojin za su iya kashe Mohamed Bazoum, yin hakan zai zama baranzana ga kasar makwabtan

Niger - Manyan sojojin kasar Nijar da su ka hambarar da gwamnatin farar hula kuma su ka dare kan mulki, su na barazanar hallaka Mohamed Bazoum.

AP ta kawo rahoto a yammacin Alhamis cewa sojojin da su ka yi juyin mulki sun nuna idan makwabta suka shigo da yaki, za a rasa Mohamed Bazoum.

Wani babban jami’in Jamhuriyyar ya sanar da karamar Sakatariyar gwamnatin Amurka, Victoria Nuland cewa ba za su yarda da katsalandan ba.

Kara karanta wannan

Juyin Mulki: Bidiyo Ya Bayyana Yayin da Asari Dokubo Ya Sha Alwashin Yin Kasa-Kasa Da Gwamnatin Sojan Nijar

Bazoum
Mohammed Bazoum a Najeriya Hoto: @mohamedbazoum
Asali: Twitter

Sojojin tawaye ba za su amince ba

Kamar yadda Nuland ta yi bayani, sojan wanda ya na cikin wadanda suka kifar da gwamnati ya yi magana ne ba tare da ya bari an kama sunansa ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Bazoum ya na tsare tun ranar 26 ga watan Yuli da aka hambarar da gwamnatinsa.

Kwanaki kadan da sauka daga karagar mulki ta hanyar nuna masa kan bindiga, tsohon shugaban Jamhuriyyar ya yi bayanin irin azabar da yake sha.

Wani shiri ECOWAS ta ke yi a Nijar?

Ko da kungiyar ECOWAS tace makasudin taron da aka yi na yau shi ne a samu zaman lafiya, a gefe guda akwai yunkurin dawo da mulkin farar hula.

Majiyar ta ce ECOWAS za su dage domin ganin Bozoum ya koma kan kujerarsa a Niamey, sojojin tawaye kuma sun shirya kashe tsohon shugaban kasar.

Kara karanta wannan

Bazoum: 'Gayar Shinkafa' Na Ke Ci Yanzu, Hambararen Shugaban Nijar Ya Koka

Shugaban hukumar ECOWAS, Omar Alieu Touray ya ce ya zama dole su yi biyayya ga umarnin dakarun sojojin yankin na shirin kai yaki a kasar Afrikar.

Bello Yabo ya saki kalamai

Kwanaki aka ji Sheikh Bello Yabo ya ce juyin mulkin da aka yi maganar cikin gidan Nijar ne ba na Najeriya ba, iyakar Bola Tinubu bada shawara kurum.

Malamin ya ce babu bambanci tsakanin Nijar da Sokoto, ya ce mutanen Nijar Musulmai ne, ya bada shawarar a addabi 'yan bindigan da ke jeji.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng