Juyin Mulki: Sojojin Nijar Sun Kulle Sararin Samaniyar Kasar

Juyin Mulki: Sojojin Nijar Sun Kulle Sararin Samaniyar Kasar

  • Gwamnatin mulkin soja ta Jamhuriyar Nijar a ƙarƙashin jagorancin Janar Abdourahamane Tchiani ta sanar da kulle sarararin samaniyar ƙasar
  • Janar Tchiani ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, 6 ga watan Agusta bayan wa'adin miƙa wuya da ECOWAS ta bayar ya cika
  • Kamar yadda yake ƙunshe a cikin sanarwar, Janar Tchiani ya yi nuni da cewa duk wani ƙoƙarin mamayar Nijar zai fuskanci martani mai ƙarfi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Niamey, Nijar - Rahotanni dake fitowa sun tabbatar da cewa gwamnatin sojin da Janar Abdourahamane Tchiani ke jagoranta a Jamhuriyar Nijar, ta kulle sararin samaniyarta a yayin da take fuskantar barazanar yin amfani da ƙarfin soji daga ƙasashen waje.

A cewar rahoton Bloomberg, hakan na zuwa ne bayan wa'adin miƙa wuya da ƙungiyar raya tattalin arziƙin ƙasashen Afirika ta Yamma (ECOWAS) suka sanya ya ƙare a ranar Lahadi, 6 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Juyin Mulkin Nijar: Shugabannin ECOWAS Sun Gana Bayan Janar Tchiani Ya Yi Biris Da Wa'adin Da Suka Ba Shi

Nijar ta kulle sararin samaniyarta
Sojojin Nijar sun kulle sararin samaniyar kasar Hoto: RTN-Tele Sahel
Asali: Getty Images

An tattaro cewa a wajen kulle sararin samaniyar ƙasar, Janar Tchiani ya yi gargaɗin cewa duk wani ƙoƙarin mamayar sararin samaniyar Nijar za su ɗauke shi a matsayin yaƙi sannan za su mayar da martani mai ƙarfi ba tare da ɓata lokaci ba.

A cewar rahoton Aljazeera, ya bayyana cewa:

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

"Fuskantar barazanar masu shiga tsakani wacce take ƙara fitowa fili ta hanyar shirye-shiryen da ƙasashe maƙwabtan mu ke yi, daga yau ranar Lahadi sararin samaniyar Nijar an kulle shi ga dukkanin jirage har sai abinda hali ya yi."

Har yanzu Shugaba Bazoum yana tsare

Shugaba Mohamed Bazoum da aka cafke har yanzu yana tsare a hannun Janar Tchiani, yayin da yake ci gaba da ƙeƙashewa wajen ƙin sakinsa ko miƙa masa mulkinsa kamar yadda ECOWAS da ƙasashen Yamma suka buƙata.

Kara karanta wannan

Fargabar Yaƙi: Jerin Jihohin Najeriya 7 da Suka Haɗa Boda da Jamhuriyar Nijar

A ranar Lahadi ta makon da ya gabata ne ƙungiyar ECOWAS ta ba sojojin juyin mulkin Nijar wa'adin sati ɗaya su sauka daga kan mulki ko ta yi amfani da ƙarfin soja a kansu.

An kifar da gwamnatin Bazoum a ranar Laraba, 26 ga watan Yuli, lokacin da mambobin dakarun dake tsaronsa suka tsare shi a cikin fadar shugaban ƙasa.

Najeriya Na Bukatar Dawo Da Daidaito a Nijar, Reno Omokri

A wani labarin kuma, tsohon hadimin shugaban ƙasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri ya yi sabon tsokaci kan juyin mulkin Jamhuriyar Nijar.

Omokri ya yi nuni da cewa dole ne Najeriya ta dawo da daidaito a Nijar domin halin rashin tabbar a ƙasar babbar barazana ce ga Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng