Juyin Mulki: Jerin Kasashen Afirka 6 Da Yanzu Haka Ke a Karkashin Mulkin Soja
Afrika ta kasance ta na fama da yawaitar juyin mulki daga sojoji tun a can baya, wanda a yanzu haka kuma yake ci gaba da gudana a sassa daban-daban na nahiyar.
Tun bayan mulkin mallakan da turawa suka gudanar, yankin Afrika ta Yamma ne ya fi fuskantar kalubale na yawaitar juyin mulki.
Hakan ba zai rasa nasaba da rashin ingantacen shugabancin da ake samu a kasashen a ƙarƙashin mulkin dimokuradiyya ba.
Ana ganin cewa mulkin farar hula a ƙasashen na Afrika, cike yake da rashawa, nuna son kai, ƙabilanci da kuma nuna bambancin addini.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Jerin ƙasashen Afrika 6 da ke karkashin mulkin soja a yanzu
A yanzu haka ƙasashen Afrika shida ne suke a ƙarƙashin mulkin soja kamar da yadda wani rahoto da jaridar Daily Trust ta wallafa ya nuna.
1. Burkina Faso
Burkina Faso na daga cikin kasashe rainon Faransa a Afrika ta Yamma.
Yawan jama'an da ke Burkina Faso ya haura miliyan 22.1 kamar yadda wani rahoto na bankin duniya ya nuna a shekarar 2021.
Kasar ta na da fadin da ya kai kilimita 274,200, sannan kuma ta yi iyaka da kasashen Mali, Nijar, Benin, Togo, Ghana da kasar Ivory Coast.
A yanzu haka kasar ta Burkina Faso na karkashin jagorancin matashin soja mai shekaru 34, wato Ibrahim Traoré, wanda ya karbi mulki a watan Janairun 2022.
2. Chad
Kasar Chadi na daga cikin kasashen Afrika da sojoji ke mulka, wacce ta yi iyaka da kasashen Libya, Sudan, Afrika ta Tsakiya, Kamaru, Najeriya da kuma Nijar.
Ta na da yawan al'umma da ya kai miliyan 17.18 a shekarar 2021, kuma suna amfani da yaran Faransanci da kuma Larabci.
Mahamat Idriss Déby ne ke shugabantar kasar tun watan Afrilun shekarar 2021.
3. Guinea
Kasar Guinea wacce ita ma rainon Faransa ce na cikin kasashen Afrika da ke a karkashin mulkin soji.
Yawan mutanen kasar bai wuce 13.53 ba, kuma kasa ce da Allah ya albarkace ta da gandun daji da ke dauke da dabbobi iri-iri.
Kasar dai a yanzu haka ta na a karkashin ikon soja mai kimanin shekaru 43 mai suna Mamady Doumbouya, wanda ya karbi mulki tun watana Satumban 2021.
4. Mali
Kasar Mali, wacce ita ma rainon Faransa ce, ta na a karkashin mulkin soja tun watan Agustan shekarar 2020.
Mali ce kasa ta takwas a fadi a Afrika, ta na da fadin kasa da ya kai kilomita 1,241,238 da kuma yawan jama'a da ya kai miliyan 21.9.
Assimi Goïta, dan shekara 42 ne sojan da yake jagorantar kasar ta Mali a yanzu haka.
5. Niger
Jamhuriyar Nijar ce kasar da sojoji suka yi wa juyin mulki a baya-bayan nan, wanda ya wakana a ranar Laraba, 26 ga watan Yulin 2023.
Nijar na daga cikin kasashen Afrika rainon kasar Faransa, wacce ta ke da yawan jama'an da suka kai miliyan 25.25.
Janaral Abdourahamane Tchiani ne dai ke jagorantar kasar a yanzu haka tun bayan kifar da gwamnatin hambararren shugaban kasar, Mohamed Bazoum.
6. Sudan
Kasar Sudan kasa ce dake a Arewacin Afrika, wacce take da yawan jama'an da ya haura miliyan 45.
Ana amfani da yaren Larabci, Nobiin da kuma Turanchi a kasar ta Sudan.
A yanzu haka kasar Sudan na karkashin mulkin Janaral Abdel Fattah al-Burhan.
Sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun yi watsi da buƙatar ECOWAS
Legit.ng a baya ta kawo muku rahoto kan fatali da buƙatar ECOWAS da sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar suka yi.
Sojojin sun kuma gargadi ƙasashen na ECOWAS da kar su kuskura su yi amfani da ƙarfin soji wajen ƙwatar mulki daga hannunsu.
Asali: Legit.ng