Dole Bazoum Ya Koma Mulki, Gwamnatin Amurka Ta Goyi Bayan Tinubu da ECOWAS

Dole Bazoum Ya Koma Mulki, Gwamnatin Amurka Ta Goyi Bayan Tinubu da ECOWAS

  • Matsayar Amurka a Nijar bayan juyin mulki ita ce dole gwamnati ta koma mulki ba tare da wata-wata ba
  • Antony J. Blinken ya goyi bayan kungiyar ECOWAS a karkashin jagorancin Shugaba Bola Ahmed Tinubu
  • Amurka ta ce a gaggauta dawo da Mohammed Bazoum, ba za ta yarda da mulkin sojoji a kasar Nijar ba

United States - Kasar Amurka ta na bibiyar abubuwan da su ke faruwa a kasar Nijar a sakamakon juyin mulkin da aka yi wa Mohammed Bazoum.

Sojoji sun hambarar da shugaban Jamhuriyyar Nijar, Mohammed Bazoum, Antony J. Blinken ya fitar da jawabai a shafin Twitter cikin makon jiya.

Sakataren gwamnatin Amurkan ya yi Allah-wadai da abin da ya faru, ya shaida cewa dole shugaban da aka tunbuke ya koma karagar mulki.

Bola Tinubu da Mohammed Bazoum
ECOWAS: Bola Tinubu da Mohammed Bazoum Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Antony J. Blinken ya tabbatar da gwamnatin Joe Biden ta na goyon bayan matsayar da kungiyar kasashen Afrika ta yamma (ECOWAS) ta dauka.

Kara karanta wannan

Ta Rikice a Nijar, Masu Zanga-Zanga Sun Farmaki Ofishin Jakadancin Faransa

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Matthew Miller ya saki jawabi

Jaridar The Nation ta ce ofishin Kakakin Sakataren gwamnatin ya fitar da jawabi na musamman daga birnin Washington DC ta bakin Matthew Miller.

Mista Miller ya ce Blinken ya damu, yana mai takaicin kifar da gwamnatin mulkin farar hula da kuma tsare shugaban kasa ba a bisa kan kai’da ba.

"Kasar Amurka ta na mai goyon bayan yunkurin Shugaban kasa Bola Tinubu na dawo da gwamnatin farar hula a jamhuriyyar Nijar.
Blinken ya godewa jagorancin Bola Tinubu a matsayin shugaban Najeriya da shugaban kungiyar ECOWAS, yayin da ake rikicin nan.
Ya na mai nuna goyon bayansa ga shugaba Tinubu kan kokarin da yake cigaba da yi na dawo da kundin tsarin mulki a jamhuriyyar Nijar.”
Ina maraba tare da goyon bayan shugannin ECOWAS na kungiyar shugabanni da gwamnatocin duka Afrika na kare tsarin mulki a Nijar.

Kara karanta wannan

Akwai sharrin Turawa: Shehu Sani ya fadi abubuwa 5 da suke sa juyin mulki a Afrika

Dole ayi gaggawar dawo da halatacciya kuma zababbiyar gwamnati a kan karagar mulki.

- Matthew Miller.

Jaridar ta ce Sakataren gwamnatin Amurkan ya ce Bola Tinubu ya nuna jagoranci bayan juyin mulkin, yana tsare marbar farar hular makwabciyarsa.

Blinken ya ce sun tattauna a game da yadda kasashen Duniya za su hada-kai, su tabbatar da an yi fatali da mulkin soja a Nijar a yammacin Afrika.

Zaben Najeriya na 2023

A shekara 73 a Duniya, Charley Boy ya ce zai fito zigidir a Legas muddin Peter Obi ya kai labari a kotu, inda ake kalubalantar nasarar Bola Ahmed Tinubu.

‘Dan takaran shugaban kasa na LP kuma jagoran ‘Yan Obidient yana karar zaben 2023 a gaban kotu, duk shi ne ya zo na uku, yana so a ba shi nasara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng