Tsohon Firayim Minista Ya Mutu Ya Bar Wa Masoyiya Gadon Naira Biliyan 85 Ita Kadai

Tsohon Firayim Minista Ya Mutu Ya Bar Wa Masoyiya Gadon Naira Biliyan 85 Ita Kadai

  • Silvio Berlusconi ya bar dukiyar da ta kai biliyan €6bn ga magada a lokacin da ya mutu a watan Yuni
  • Wasiyya ta nuna masoyiyar ‘dan siyasar watau Marta Fascina za ta tashi da €100m daga cikin dukiyarsa
  • Tsohon Firayim Ministan ya yi mulki a kasar Italiya, kuma ya na cikin fitattun ‘yan kasuwan da aka yi

DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!

Italiya – Tsohon Firayim Ministan Italiya, Marigayi Silvio Berlusconi ya bar €100m (£85.4m) daga tarin dukiyarsa ga Marta Fascina bayan rasuwarsa.

The Guardian ta kawo rahoto dazu cewa wasiyyar da Silvio Berlusconi ya bari ita ce masoyiyar ta shi za ta ci gadon makudan kudin da ya bari a Duniya.

Sannan Marta Fascina za ta samu hannun jari mai tsoka a kamfanin dangin Berlusconi, Fininvest. Matar za tayi tarayya da 'ya 'yan marigayin.

Kara karanta wannan

Asalin Abin da Ya Kai Ni Wajen Tinubu a Aso Rock – ‘Dan Takaran Shugaban Kasa a PDP

Silvio Berlusconi
Silvio Berlusconi da Marta Fascina Hoto: www.open.online
Asali: UGC

Berlusconi ya mutu ya bar Berlusconi €6bn

Marigayin wanda ya yi Firayim Minista sau uku a kasar Italiya ya rasu kwanakin baya, ya bar dukiya da kadarorin da sun kai na fam biliyan €6bn.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Majiyar ta ce kanin Berlusconi mai suna Paolo zai samu €100m a cikin gado, sai kuma wani abokin siyasarsa, Marcello Dell’Utri ya samu €30m.

Marcello Dell’Utri ya taba zama Sanata a karkashin jam’iyyar Forza Italia kuma ya na cikin wadanda su ka yi zaman gidan yari tare da mai rasuwan.

Wasiyyar da attajirin ya bari kuwa ya yankawa ‘ya ‘yansa - Marina da Pier Silvio da kuma matarsa ta farko Carla Elvira Dall’Oglio, 53% na hannun jari.

Marigayi ya bar wasiyyar gado

Rahoton BBC ya ce Marigayin ya yi kason a wata wasiyya da ya rubuta da hannunsa a wata takarda mai ruwan kwai a gidansa a Villa San Martino.

Kara karanta wannan

‘Dan Kwankwasiyya Mai Goyon Bayan Rusau Ya Koma Salati, Rushe-Rushe Ya Zo Kan Shi

An rubuta wasilar ne tun Oktoban 2022 a lokacin da jam’iyyarsa ta ke shirin komawa mulki.

Fascina mai shekara 33 a Duniya ta rike kujerar mataimakiyar shugabar jam’iyyar Forza Italia, a lokacin yana gadon mutuwa an ji ya kira ta da matarsa.

Daga baya aka ji labari ta na soyayya da tsohon Firayin Ministan a 2020, lamarin da ya kai suka yi wani irin auren je-ka-na-yi a farkon shekarar 2020.

Gwamnan jihar Sokoto

An samu labari cewa da direbobi su ka batawa Gwamnan jihar Sokoto lokaci, sai ya tuko kan shi zuwa zuwa ofis da sassafe a lokacin mutane na barci.

Da Gwamna Ahmad Aliyu ya shigo ofis, bai samu kowa ba sai ma’aikata uku, nan-take ya ce a rufe kofar shigowa, daga ciki har da hadimansa a waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng