Mataimakin Buhari, Farfesa Osinbajo Ya Samu Aikin Farko Bayan Barin Aso Rock
- Jirgin Yemi Osinbajo ya sauka a kasar Sierra Leone yayin da ake shirin yin zaben shugabannin bana
- Tsohon mataimakin shugaban Najeriya ne jagoran kungiyar Commonwealth da za ta sa ido a zabukan
- A karshen watan Mayun nan Farfesa Osinbajo ya sauka daga mulki, ya yi shekaru 8 a Aso Rock Villa
Sierra Leone - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo ya tafi Sierra Leone a karshen makon nan domin aikin zaben da za a shirya a kasar.
Kamar yadda ya fadi a shafinsa, Farfesa Yemi Osinbajo zai jagoranci tawagar kungiyar Commonwealth (COG), domin sa ido a zaben da za ayi.
Osinbajo ya amince ya yi aikin lura da zaben ne makonni uku da sauka daga kujerar shugaban kasa a Najeriya inda ya yi shekaru takwas a kan mulki.
Wannan ne kusan muhimman aikin farko da Farfesa Osinbajo ya yi bayan barin ofis a Mayu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Zuwa S/Leone a ranar Asabar
Punch ta ce Sakatare Janar na kungiyar COG mai lura da harkokin zabe, Patricia Scotland ta kaddamar da kwamitin da Farfesan yake jagoranta.
Sauran abokan aikinsa sun kunshi mutum 11 wanda za su sa ido a kan yadda aka gudanar zabukan bana domin aba kungiyar cikakken rahoto.
A rana ta biyu da isansa kasar, Farfesan ya tabbatar da ya yi zama na musamman kuma ya tattauna da Scotland da sauran ‘yan kungiyar ta sa.
Osinbajo a kasar Norway
Kafin nan, Osinbajo ya halarci wani taro da gwamnatin Norway ta shirya a birnin Oslo a makon jiya, bayan zaman ne aka yi kayatacciyar liyafa.
Taron ya ba shi damar haduwa da tsohon shugaban kasar Afrika ta Kudu, Ministocin kasashen Somaliya da Columbiya da wasu manyan Duniya.
Laolu Akande ya yi magana a Twitter, ya ke cewa mai gidansa zai kasance a kasar Afrikan na tsawon wannan wata na Yuni domin wannan aiki.
Za ayi zabe na biyar a S/Leonne
Akande ya ce tsohon mataimakin shugaban na Najeriya zai yi wa manema labarai jawabi a ranar Litinin, a karshen wata zai gabatar da rahoton COG.
Wannan ne karo na biyar da kungiyar renon kasashen Afrikar ta ke sa ido a kan zabukan Sierra Leone tun bayan kawo karshen yakin basasa a 2022.
Nada Ministocin Najeriya
A rahoton da mu ka fitar a farkon makon nan, an ji manyan ‘yan siyasa sun koma zagayen Aso Rock saboda su samu mukami a gwamnati mai-ci.
Bola Tinubu ya na kokarin jawo ‘yan adawa, hakan bai yi wa wasu ‘Yan APC dadi. Wasu tsofaffin gwamnonin jihohi su na neman zama Minsitoci.
Asali: Legit.ng