Shugaban INEC Yakubu, Wike, Uzodinma, Na Cikin Wadanda Aka Haramtawa Shiga USA? Gwamnatin Amurka Ta Magantu

Shugaban INEC Yakubu, Wike, Uzodinma, Na Cikin Wadanda Aka Haramtawa Shiga USA? Gwamnatin Amurka Ta Magantu

  • An yi ta yaɗa jerin sunayen wasu ‘yan Najeriya da aka ce an haramtawa zuwa Amurka saboda kawo cikas a zaɓen 2023 a shafukan sada zumunta
  • Ofishin jakadancin Amurka da ke Najeriya, ya yi martani kan jerin sunayen da ya karaɗe intanet, inda ya bayyana shi a matsayin cewa na bogi ne
  • Ofishin jakadancin ya ce ba ya fitar da sunayen mutanen da aka haramtawa biza, ya ƙara da cewa bayanan biza na mutum abu ne na sirri ne, kamar yadda dokar Amurka ta tanada

FCT, Abuja - Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya ya ce jerin sunayen 'yan Najeriya da aka ce an haramtawa biza na bogi ne.

Ofishin jakadancin Amurka da ke Najeriya ya ce ba daga wurinsa jerin sunayen mutanen ya fito ba, sannan kuma bayanan biza na mutum abu ne na sirri ne, kamar yadda dokar Amurka ta tanada, in ji rahoton labaran BBC sashen Pidgin.

Kara karanta wannan

Shugaban NNPC Kyari, Ya Bayyana Babban Dalilin Da Ya Sa Dole a Cire Tallafin Man Fetur

Amurka ta yi magana kan mutanen da aka ce ta haramtawa biza
Gwamnatin Amurka ta karyata batun haramcin biza kan wasu 'yan Najeriya da aka ce ta yi. Hoto: Hope Uzodimma, Alhaji Musiliu Mc Oluomo, Press Unit - Rivers State Government House, INEC Nigeria
Asali: Facebook

Mutanen da aka ambata a haramcin bizar ta Amurka

Wani ɗan a mutun Peter Obi, ɗan takarar shugabancin ƙasa a jam’iyyar Labour a zaɓen 2023, @PeterObiUSA ne ya wallafa jerin sunayen a shafinsa na Tuwita.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya yi iƙirarin cewa jerin sunayen na ɗauke da mutanen da wata kungiyar fafutukar dimokuraɗiyya ta ‘yan Najeriyar mazauna Amurka (NACJD), ta miƙawa mahukunta ƙasar.

Ya yi ikirarin cewa, a yayin wata zanga-zanga ranar Litinin, 3 ga watan Afrilu, 2023, a fadar White House da majalisar dokokin Amurka a Washington DC ne suka mika sunayen.

Mutumin ya wallafa a shafinsa na Tuwita, a ranar Litinin, 15 ga watan Mayu, sunayen mutanen da ya kira waɗanda suka aikata maguɗin zaɓe da suka haɗa da Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas, gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, da shugaban 'yan kamashon jihar Legas (LASPG), Musiliu Akinsanya, wanda aka fi sani da MC Oluomo.

Kara karanta wannan

Manajan NNPC, Mele Kyari Ya Yi Bayani Dangane Da Farashin Da Ake Siyan Man Fetur Yanzu a Kasuwa

Rubutun da @PeterObiUSA ɗin ya yi, ya samu mutane aƙalla dubu 500 da suka karanta shi, da kuma sama da 2000 da suka sake yaɗa shi. Sai dai Ofishin jakadancin Amurka a Najeriya, ya yi watsi da jerin sunayen.

Shahararren mai fafutuka ya ƙalubalanci Amurka da ta sanya sunayen waɗanda aka haramtawa biza

Da yake mayar da martani kan batun, mai fafutukar yaƙi da cin hanci, Hamzat Lawal, ya buƙaci Amurka da ta buga sunayen waɗanda ta sanya wa takunkumin hana shiga ƙasarta saboda laifukan zaɓe.

A hirarsa da gidan Talabijin na Channels a ranar Litinin, 15 ga watan Mayu, Lawal ya ce, 'yan Najeriya da dama na tsammanin cewa rundunar ‘yan sandan Najeriya, za ta hukunta duk waɗanda suka yi katsalandan a harkokin zaɓe.

Da gaske ne ɗan Shugaban hukumar zaɓe ya haukace a Saudiyya

Tun bayan kammala zaɓen 2023 da ya gabata ne akai ta yaɗa wani labari a kafafen sada zumunta, dangane da iyalan shugaban hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu.

Kara karanta wannan

Cire Tallafin Man Fetur: Reno Omokri Ya Lissafa Muhimman Sharudda 4 Da Ya Kamata Gwamnatin Tinubu Ta Cika

A rubutun wanda ya yaɗu sosai a soshiyal midiya, an bayyana cewa ɗan Farfesa Yakubu ya haukace a Saudiyya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Deen Dabai avatar

Deen Dabai Zaharaddeen Hamisu marubuci kuma ma'aikacin jarida ne da ke da gogewa wajen iya tantance sahihan labarai da na karya. Ya yi digirinsa a jami'ar Ahmadu Bello dake Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Baya ga haka, ya shafe sama da shekaru 5 a bangaren aikin watsa labarai wanda hakan ya bashi gogewa ta musamman a aikin jarida. Za a iya tuntubarsa ta adireshinsa na yanar gizo: deen.dabai@corp.legit.ng